Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Sarakuna 16:7 - Littafi Mai Tsarki

7 Ubangiji kuma ya yi magana da Yehu ɗan Hanani, a kan Ba'asha da gidansa, saboda muguntar da ya aikata a gaban Ubangiji, har ya sa Ubangiji ya yi fushi, gama abin da ya aikata ya yi daidai da na Yerobowam, saboda kuma ya hallaka gidan Yerobowam.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

7 Ban da haka, maganar Ubangiji ta zo ta wurin annabi Yehu ɗan Hanani wa Ba’asha da gidansa, saboda dukan muguntar da ya aikata a gaban Ubangiji, ya tsokane shi yă yi fushi ta wurin abubuwan da ya yi, da kuma zama kamar gidan Yerobowam, da kuma domin ya hallaka gidan Yerobowam.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Sarakuna 16:7
15 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ubangiji kuwa ya ce masa, “Ka raɗa masa suna, Yezreyel, gama ba da daɗewa ba zan ziyarci gidan Yehu da hukunci saboda jinin da ya zubar a Yezreyel. Zan sa mulkin Isra'ila ya ƙare.


Ƙasarsu tana cike da gumaka, suna sujada ga abubuwan da suka yi da hannuwansu.


Amma nasu alloli na azurfa da zinariya ne, Da hannu aka siffata su.


Ubangiji kuma zai ta da wani wanda zai sarauci Isra'ila, wanda kuma zai rushe gidan Yerobowam daga yanzu har zuwa nan gaba.


shi Yesun nan fa, an ba da shi bisa ƙaddarar Allah da rigyasaninsa, ku kuwa kuka gicciye shi, kuka kashe shi, ta hannun masu zunubi.


Kada ka rusuna musu, kada kuwa ka bauta musu, gama ni Ubangiji Allahnka, mai kishi ne. Nakan hukunta 'ya'ya har tsara ta uku da ta huɗu na waɗanda suke ƙina.


A shekara ta ashirin da shida ta sarautar Asa, Sarkin Yahuza, Ila ɗan Ba'asha, ya ci sarautar Isra'ila a Tirza. Ya yi sarauta shekara biyu.


Amma Ubangiji ya faɗakar da jama'ar Isra'ila da jama'ar Yahuza ta bakin annabawa da kowane maigani, cewa su bar mugayen hanyoyinsu, su kiyaye umarnansa da dukan dokokinsa waɗanda ya umarci kakanninsu da su, waɗanda kuma ya aiko musu ta wurin bayinsa annabawa.


A lokacin nan sai Hanani, maigani, ya zo wurin Asa, Sarkin Yahuza, ya ce masa, “Da yake ka dogara ga Sarkin Suriya, maimakon ka dogara ga Ubangiji Allahnka, shi ya sa rundunar sojojin Sarkin Suriya ta kuɓuta daga hannunka.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ