32 Ya gina wa Ba'al bagade a matsafar Ba'al ɗin, da ya gina a Samariya.
32 Ya kafa bagade domin Ba’al a haikalin Ba’al da ya gina a Samariya.
sai ya aika cikin Isra'ila duka, dukan masu yi wa Ba'al sujada kuwa suka zo, ba wanda bai zo ba. Suka shiga, suka cika haikalin Ba'al makil daga wannan gefe zuwa wancan.
Ya aikata mugun abu a gaban Ubangiji, amma bai kai na tsohonsa da tsohuwarsa ba, gama ya kawar da ginshiƙin gunkin nan Ba'al wanda tsohonsa ya yi.
Yehu kuwa ya tara mutane duka, ya ce musu, “Ahab ya bauta wa Ba'al kaɗan, amma Yehu zai bauta masa da yawa.
Iliya kuwa ya amsa ya ce, “Ban wahalar da Isra'ila ba, kai ne da tsohonka, gama kuna ƙin bin umarnan Ubangiji, kuna yi wa Ba'al sujada.