Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Sarakuna 16:12 - Littafi Mai Tsarki

12 Haka Zimri ya hallaka gidan Ba'asha bisa ga maganar da Ubangiji ya faɗa a kansa ta bakin annabi Yehu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

12 Ta haka Zimri ya hallaka dukan iyalin Ba’asha, bisa ga maganar da Ubangiji ya yi game da Ba’asha ta wurin annabi Yehu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Sarakuna 16:12
11 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ubangiji ya yi magana da Yehu, ɗan Hanani a kan Ba'asha, ya ce,


Mutumin da ya sa wawa ya isar masa da saƙo ya datse ƙafafunsa, yana nemar wa kansa wahala.


Sarki bai kasa kunne ga jama'ar ba, gama wannan al'amari, Allah ne ya aukar da shi, domin ya cika maganar da ya faɗa wa Yerobowam ɗan Nebat, ta bakin Ahaija Bashilone.


Ya kafa iyakar Isra'ila daga ƙofar Hamat har zuwa tekun Araba. Wannan kuwa shi ne abin da Ubangiji, Allah na Isra'ila, ya faɗa ta bakin bawansa annabi Yunana, ɗan amittai, daga Gathefer.


Ubangiji kuma ya yi magana da Yehu ɗan Hanani, a kan Ba'asha da gidansa, saboda muguntar da ya aikata a gaban Ubangiji, har ya sa Ubangiji ya yi fushi, gama abin da ya aikata ya yi daidai da na Yerobowam, saboda kuma ya hallaka gidan Yerobowam.


to, zan shafe ka da gidansa, in mai da gidanka kamar gidan Yerobowam ɗan Nebat.


Jama'ar Isra'ila duka suka binne shi, suka yi makoki dominsa, kamar yadda Ubangiji ya faɗa ta bakin bawansa, annabi Ahija.


Aka yi ta yaƙi tsakanin Asa da Ba'asha, Sarkin Isra'ila a dukan kwanakin mulkinsu.


Sai Yehu maigani, ɗan Hanani, ya fita domin ya tarye shi, ya ce wa sarki Yehoshafat, “Za ka taimaki mugu ka kuma ƙaunaci maƙiyan Ubangiji? Saboda haka hasalar Ubangiji za ta same ka.


Sauran ayyukan Yehoshafat, daga farko zuwa ƙarshe, an rubuta su a littafin tarihin Yehu ɗan Hanani, wanda aka rubuta a littafin sarakunan Isra'ila.


Garin da yake cikin tukunyar bai ƙare ba, kamar yadda Ubangiji ya faɗa ta bakin Iliya.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ