21 Da Ba'asha ya ji labari, sai ya daina ginin Rama, ya tafi ya zauna a Tirza.
21 Da Ba’asha ya ji haka, sai ya daina ginin Rama, ya janye zuwa Tirza.
Sa'an nan matar Yerobowam ta tashi, ta tafi Tirza. Amma tana shiga gidan ke nan, sai yaron ya mutu.
Ƙaunatacciyata, kina kyakkyawa kamar Urushalima, Kyakkyawa kuma kamar birnin Tirza, Kina da shiga rai kamar ɗaya daga cikin biranen nan.
Da Ba'asha ya ji haka, sai ya daina gina Rama, ya bar aikin da yake yi.
Ba'asha, Sarkin Isra'ila, ya kai wa Yahuza yaƙi. Sai ya gina Rama don ya hana kowa ya fita ko kuma ya shiga wurin Asa, Sarkin Yahuza.
Ba'asha kuwa ya rasu, aka binne shi a Tirza. Sai Ila, ɗansa ya gāji sarautarsa.
A shekara ta talatin da ɗaya ta sarautar Asa, Sarkin Yahuza, Omri ya ci sarautar Isra'ila. Ya yi shekara goma sha biyu yana sarauta. Ya yi shekara shida yana mulki a Tirza.