Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Sarakuna 15:20 - Littafi Mai Tsarki

20 Ben-hadad kuwa ya yarda da maganar sarki Asa. Ya kuwa aiki shugabannin sojojinsa su yi yaƙi da garuruwan Isra'ila. Su kuwa suka tafi, suka ci Iyon, da Dan, da Abel-bet-ma'aka, da dukan Kinneret, da dukan ƙasar Naftali.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

20 Ben-Hadad ya yarda da maganar Sarki Asa, ya kuma aika shugabannin sojojin mayaƙansa ya yi yaƙi da garuruwan Isra’ila. Ya kame Iyon, Dan, Abel-Bet-Ma’aka da dukan Kinneret, haɗe da Naftali.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Sarakuna 15:20
10 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

A zamanin Feka Sarkin Isra'ila, sai Tiglat-filesar mai mulkin Assuriya, ya zo ya ci Iyon, da Abel-bet-ma'aka, da Yanowa, da Kedesh, da Hazor, da Gileyad, da Galili, da dukan ƙasar Naftali. Sa'an nan ya kwashe mutane zuwa bauta a Assuriya.


Suka sa wa birnin suna Dan, ɗan Yakubu. Kafin wannan lokaci kuwa ana kiran birnin Layish ne.


da sarakunan da suke arewacin ƙasar tuddai, da cikin Araba a kudancin Kinneret, da cikin filayen kwari, da cikin Dor a yamma.


Ya kafa siffar maraƙi ɗaya a Betel, ɗayan kuma a Dan.


daga kuma Araba zuwa gabashin Tekun Kinneret da zuwa Tekun Araga, wato Tekun Gishiri, a wajen gabas ta hanyar Ber-yeshimot, da wajen kudu zuwa gangaren gindin Dutsen Fisga,


Lokacin da Abram ya ji an kama danginsa wurin yaƙi sai ya shugabanci horarrun mutanensa, haifaffun gidansa, su ɗari uku da goma sha takwas, suka bi sawun sarakunan har zuwa Dan.


Ben-hadad Sarkin Suriya kuwa ya tara dukan sojojinsa. Sarakuna talatin da biyu kuma suna tare da shi, da dawakai, da karusai. Ya haura ya kai wa Samariya yaƙi. Ya kuwa yi yaƙi da ita.


Ben-hadad ya ce masa, “Biranen da tsohona ya ƙwace daga wurin tsohonka, zan mayar maka. Kai kuma za ka yi karauku a Dimashƙu kamar yadda tsohonka ya yi a Samariya.” Sai Ahab ya ce, “Zan bar ka, ka tafi a kan wannan sharaɗi.” Ya kuwa yi alkawari da shi, sa'an nan ya bar shi, ya tafi.


Waɗannan garuruwa da ƙauyukansu su ne rabon gādon kabilar Naftali da iyalanta.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ