Ubangiji ya ce, “Kada ku haura zuwa yaƙi da 'yan'uwanku, mutanen Isra'ila, sai kowa ya koma gidansa, gama wannan al'amari daga wurina ne.” Su kuwa suka yi biyayya da maganar Ubangiji, suka koma gida.
Da Rehobowam ya komo Urushalima, sai ya tara dukan jama'ar gidan Yahuza, da na kabilar Biliyaminu. Aka sami mayaƙa dubu ɗari da dubu tamanin (180,000) waɗanda za su yi yaƙi da gidan Isra'ila, don su komar da su a ƙarƙashin mulkin Rehobowam, ɗan Sulemanu.
Ayyukan Rehobowam, daga farko har zuwa ƙarshe an rubuta su a littafin tarihin annabi Shemaiya, da na Iddo maigani. Kullum yaƙi ne tsakanin Rehobowam da Yerobowam.