Ya ce wa sarki, “Ubangiji ya ce, ‘Domin ka aiki manzanni su yi tambaya wurin Ba'alzabul, gunkin Ekron, ba Allah a Isra'ila ne wanda za ka yi tambaya a wurinsa? Domin haka ba za ka sauko daga kan gadon da kake kwance ba, amma za ka mutu lalle.’ ”
Suka ce masa, “Wani mutum ya sadu da mu, ya ce mana, mu koma wurinka mu shaida maka, ‘Ubangiji ya ce, ba Allah a Isra'ila, har aka aike ku ku tambayi Ba'alzabul, gunkin Ekron? Domin haka ba za ka tashi daga kan gadon da kake kwance ba, amma lalle za ka mutu.’ ”
Dukan jama'ar Isra'ila za su yi makoki dominsa, su binne shi, gama shi kaɗai zai sami binnewa daga cikin gidan Yerobowam, domin a gare shi kaɗai aka iske abin da Ubangiji, Allah na Isra'ila, yake murna da shi.