Kada ka rusuna musu, kada kuwa ka bauta musu, gama ni Ubangiji Allahnka, mai kishi ne. Nakan hukunta 'ya'ya har tsara ta uku da ta huɗu na waɗanda suke ƙina.
Yerobowam kuwa ya ce wa matarsa, “Ki tashi, ki ɓad da kama don kada a sani ke matata ce, sa'an nan ki tafi Shilo wurin Ahija, annabin nan wanda ya ce mini zan sarauci jama'an nan.
Sarki Zadakiya ya aika a kawo masa Irmiya. Sarki kuwa ya shigar da shi gidansa, ya tambaye shi a asirce, ya ce, “Ko akwai wata magana daga wurin Ubangiji?” Sai Irmiya ya ce, “Akwai kuwa!” Ya ci gaba ya ce, “Za a ba da kai a hannun Sarkin Babila.”