Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Sarakuna 13:34 - Littafi Mai Tsarki

34 Wannan zunubi ya zama sanadi ga gidan Yerobowam, har ya isa a shafe gidan, a hallaka shi ƙaƙaf.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

34 Wannan ne zunubin gidan Yerobowam da ya kai ga fāɗuwarsa da kuma hallakarsa daga fuskar duniya.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Sarakuna 13:34
17 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Saboda haka zan kawo masifa a gidanka. Zan datse maka kowane ɗa namiji, ko bawa, ko 'yantacce, daga cikin Isra'ila. Zan ƙone gidanka kamar yadda akan ƙone juji ƙurmus.


Wannan abu ya zama zunubi, gama mutane sun tafi wurin siffofin maruƙan nan a Betel da Dan.


Sa'ad da Ubangiji ya ɓalle Isra'ila daga gidan Dawuda, sai suka naɗa Yerobowam ɗan Nebat ya zama sarki. Yerobowam kuwa ya karkatar da jama'ar Isra'ila daga bin Ubangiji. Ya sa su suka aikata babban zunubi.


Adalci yakan kiyaye marasa laifi, amma mugunta ita ce fāɗuwar masu zunubi.


Amma Yehu bai mai da hankali ya yi tafiya a tafarkin Ubangiji Allah na Isra'ila da zuciya ɗaya ba. Bai rabu da zunuban Yerobowam ba, wanda ya sa Isra'ila su yi zunubi.


Yerobowam kuwa ya ce a zuciyarsa, “Mulkin fa zai koma gidan Dawuda.


A lokacin nan Abaija ɗan Yerobowam ya kwanta ciwo.


Ubangiji zai rabu da Isra'ila saboda zunuban Yerobowam waɗanda ya yi, da kuma waɗanda ya sa mutanen Isra'ila su yi.”


Ya yi wa Ubangiji zunubi kamar yadda tsohonsa ya yi, ya kuma sa Isra'ila su yi zunubi.


Zan sa gidanka ya zama kamar gidan Yerobowam ɗan Nebat, da gidan Ba'asha ɗan Ahija saboda ka sa ni in yi fushi, ka kuma sa mutanen Isra'ila suka yi zunubi.’


Amma bai rabu da zunubin Yerobowam ɗan Nebat ba, wanda ya sa Isra'ila su yi zunubi. Siffofin maruƙa biyu suna nan a Betel da Dan.


Saboda haka, in ji Ubangiji, ‘Zan kawar da kai daga duniya. Za ka mutu a wannan shekara domin ka kuta tayarwa ga Ubangiji.’ ”


Za a hallaka masujadan tuddai na Awen inda Isra'ila suke yin zunubi, Ƙayayuwa da sarƙaƙƙiya za su yi girma a bagadansu. Za su ce wa manyan duwatsu, “Ku rufe mu!” Su ce wa tuddai, “Ku faɗo bisa kanmu!”


Ki koma, ki faɗa wa Yerobowam, Ubangiji Allah na Isra'ila ya ce, ‘Na ɗaukaka ka daga cikin mutane, na sa ka zama shugaban mutanena, Isra'ilawa.


Duk wanda yake naka wanda zai mutu a birni, karnuka za su cinye shi. Wanda kuma ya mutu a saura tsuntsaye za su cinye shi, ni Ubangiji, ni ne na faɗa.’


Nadab ɗan Yerobowam ya ci sarautar Isra'ila a shekara ta biyu ta sarautar Asa Sarkin Yahuza. Ya yi sarautar Isra'ila shekara biyu.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ