1 Sarakuna 12:6 - Littafi Mai Tsarki6 Sarki Rehobowam kuwa ya nemi shawara daga wurin dattawa, waɗanda suka bauta wa tsohonsa, Sulemanu, lokacin da yake da rai. Ya ce musu, “Wace shawara za ku ba ni don in amsa wa mutanen nan?” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20206 Sai Sarki Rehobowam ya nemi shawarar dattawa waɗanda suka yi wa mahaifinsa Solomon, hidima a kwanakinsa. Ya ce, “Wace shawara ce za ku ba ni don in amsa wa waɗannan mutane?” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
waɗannan kuma su ne manyan fādawansa, Azariya ɗan Zadok shi ne firist. Elihoref da Ahija 'ya'yan Seraiya, maza, su ne magatakarda. Yehoshafat ɗan Ahilud shi ne mai lura da takardu. Benaiya ɗan Yehoyada shi ne shugaban sojoji. Zadok da Abiyata su ne firistoci. Azariya ɗan Natan shi ne shugaban hakimai. Zabud ɗan Natan shi ne mashawarcin sarki da abokinsa. Ahishar shi ne mai lura da bayin fāda. Adoniram ɗan Abda, shi ne mai lura da aikin gandu.