Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Sarakuna 12:28 - Littafi Mai Tsarki

28 Sai sarki Yerobowam ya yi shawara, ya siffata 'yan maruƙa biyu da zinariya. Sa'an nan ya ce wa jama'arsa, “Zuwanku Urushalima ya isa, yanzu ga allolinku, ya Isra'ilawa, waɗanda suka fito da ku daga ƙasar Masar.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

28 Bayan ya nemi shawara, sai sarki ya yi siffofin ’yan maruƙa biyu na zinariya. Ya ce wa mutane, “Kun daɗe kuna haurawa zuwa can Urushalima. Ga allolinku, ya Isra’ila, waɗanda suka fitar da ku daga ƙasar Masar.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Sarakuna 12:28
34 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Suka bar dukan umarnan Ubangiji Allahnsu, suka yi wa kansu siffofin zubi na 'yan maruƙa biyu, suka yi gunkiyan nan, Ashtoret, suka yi wa taurari sujada, suka bauta wa Ba'al.


Amma bai rabu da zunubin Yerobowam ɗan Nebat ba, wanda ya sa Isra'ila su yi zunubi. Siffofin maruƙa biyu suna nan a Betel da Dan.


Sun yi saurin kaucewa daga hanyar da na umarce su. Sun yi wa kansu ɗan maraƙi na zubi, sun yi masa sujada, sun miƙa masa hadaya, sun kuma ce, ‘Ya Isra'ila, wannan shi ne allahn da ya fisshe ka daga ƙasar Masar’ ”


Ya karɓi zobban a hannunsu, sai ya narkar da su, ya sassaƙa shi da kurfi, ya siffata ɗan maraƙi. Da jama'a suka gani, sai suka ce, “Allahnku ke nan, ya Isra'ila, wanda ya fisshe ku daga Masar.”


Sai Yerobowam ya naɗa firistoci don masujadansa, saboda siffofin bunsurai, da na maruƙa, waɗanda ya yi.


suna yi musu alkawarin 'yanci, ga shi kuwa, su da kansu bayin zamba ne. Don mutum bawa ne na duk abin da ya rinjaye shi.


Sukan faɗa wa annabawa su yi shiru. Sukan ce, “Kada ku yi mana magana a kan abin da yake daidai. Ku faɗa mana abin da muke so mu ji ne kawai. Bari mu ci gaba da ruɗewarmu.


Ubangiji ya yi magana, ya ce, “Waɗanda suke mulkin Yahuza sun shiga uku, domin sun tayar mini. Suna aiki da shirye-shiryen da ba ni ne na yi ba, suka sa hannu a kan yarjejeniya gāba da nufina. Suna ta aikata zunubi a kan zunubi.


“Kada ka yi wa kanka wani gunki ko kuwa wata siffa ta wani abu a sama a bisa, ko a duniya a ƙasa, ko kuma a ruwa a ƙarƙarshin ƙasa.


Zo, mu san irin dabarar da za mu yi musu, don kada su riɓaɓɓanya, domin in aka faɗa mana da yaƙi, kada su haɗa kai da maƙiyanmu, su yaƙe mu, su tsere daga ƙasar.”


Musa ya ga jama'ar sun sangarce, domin Haruna ya sa su sangarce, ya bar su su bauta wa gunki har suka zama abin kunya a gaban magabtansu.


Amma ka aikata mugunta fiye da dukan waɗanda suka riga ka, ka yi wa kanka gumaka, da siffofi na zubi, ka tsokane ni in yi fushi, ka yi watsi da ni.


Ya yi wa Ubangiji zunubi kamar yadda tsohonsa ya yi, ya kuma sa Isra'ila su yi zunubi.


Wannan ya faru saboda zunuban da ya aikata, ya yi mugun abu a gaban Ubangiji, ya bi hanyar Yerobowam da zunubinsa da ya aikata, har ya sa Isra'ilawa su yi zunubi.


Sai Lawiyawa suka bar makiyayarsu da dukiyarsu, suka koma Yahuza da Urushalima, saboda Yerobowam da 'ya'yansa maza sun hana su yi hidimarsu ta firistocin Ubangiji.


Yanzu kuma, so kuke ku ƙi mulkin Ubangiji wanda yake hannun 'ya'yan Dawuda, maza, saboda yawan da kuke da shi, da gumakan maruƙan zinariya da kuke da su, waɗanda Yerobowam ya yi muku.


Isra'ila kuwa ta daɗe ba ta bin Allah na gaskiya, ba ta da firist mai koya mata, ba ta kuma bin shari'a.


Ya nemi Allah na ubansa, ya bi umarnansa. Bai bi halin Isra'ila ba.


Ya yi yadda sarakunan Isra'ila suka yi, kamar yadda gidan Ahab ya yi, gama matarsa 'yar Ahab ce. Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji.


Ba ta bar karuwancinta ba, wanda ta yi tun tana a Masar, gama a lokacin 'yan matancinta mutane sun kwana da ita, sun rungumi ƙirjinta, suka biya kwaɗayinsu a kanta.


Sarki Nebukadnezzar ya yi gunki na zinariya wanda tsayinsa kamu sittin ne, fāɗinsa kuma kamu shida. Ya kafa shi a filin Dura wanda yake a lardin Babila.


Za a hallaka masujadan tuddai na Awen inda Isra'ila suke yin zunubi, Ƙayayuwa da sarƙaƙƙiya za su yi girma a bagadansu. Za su ce wa manyan duwatsu, “Ku rufe mu!” Su ce wa tuddai, “Ku faɗo bisa kanmu!”


Kada ku tafi ku yi sujada a Biyer-sheba. Kada ku yi ƙoƙarin nemana a Betel, Gama Betel lalacewa za ta yi. Kada ku tafi Gilgal, Gama an ƙaddara wa jama'arta su yi ƙaura.”


Waɗanda suka yi rantsuwa da gumakan Samariya, Waɗanda suka ce, ‘Na rantse da gunkin Dan, Da ran gunkin Biyer-sheba,’ Irin waɗannan mutane za su fāɗi, Ba za su ƙara tashi ba.”


Dawuda ya yi tunani a ransa, ya ce, “Wata rana Saul zai kashi ni, don haka ba abin da ya fi mini, sai in tsere zuwa ƙasar Filistiyawa. Sa'an nan Saul zai fid da zuciya ga nemana a ƙasar Isra'ila. Zan kuwa tsira daga hannunsa.”


Suka bi al'adun al'ummai waɗanda Ubangiji ya kora a gabansu, da al'adun da sarakunan Isra'ila suka kawo.


Sai ya kafa gunkin da ya yi a cikin Haikalin Allah, wanda Allah ya faɗa wa Dawuda da ɗansa Sulemanu ya ce, “A cikin wannan Haikali da a Urushalima, inda na zaɓa daga cikin dukan kabilan Isra'ila, zan sa sunana har abada.


Hanyar da kake tsammani ita ce daidai, za ta kai ka ga hallaka.


Kin yi karuwanci da Masarawa, maƙwabtanki masu kwaɗayi. Kin yawaita karuwancinki don ki tsokani fushina.


Zan fāɗa wa waɗannan mutane masu zunubi, in hukunta su. Za a tattara al'ummai, su yi gāba da su, Za a hukunta su saboda yawan zunubansu.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ