Sa'ad da ta isa wurin annabi Elisha a kan dutsen, sai ta kama ƙafafunsa. Sai Gehazi ya zo zai ture ta. Amma mutumin Allah ya ce masa, “Ƙyale ta kurum, gama tana da baƙin ciki ƙwarai, Ubangiji kuwa ya ɓoye mini abin.”
Sai ta kama hanya, ta tafi wurin annabi Elisha a Dutsen Karmel. Sa'ad da annabi Elisha ya gan ta zuwa, sai ya ce wa Gehazi, wato baransa, “Duba, ga Bashunemiya can.
Akwai wani tsohon annabi a Betel. 'Ya'yansa maza kuwa suka tafi suka faɗa masa dukan abin da annabin Allah ya yi a Betel a wannan rana. Suka faɗa wa mahaifinsu maganar da annabin Allah ya faɗa wa sarki.
Amma sa'ad da Elisha, annabin Allah, ya ji cewa Sarkin Isra'ila ya keta tufafinsa, sai ya aika wa sarki ya ce, “Me ya sa ka keta tufafinka? Bari ya zo wurina, zai sani akwai annabi a Isra'ila.”
Na kawo su cikin Haikalin Ubangiji, a ɗakin 'ya'yan Hanan da Igdaliya, mutumin Allah. Ɗakin yana kusa da na shugabanni, a kan ɗakin Ma'aseya ɗan Shallum mai tsaron bakin ƙofa.
Ayyukan Rehobowam, daga farko har zuwa ƙarshe an rubuta su a littafin tarihin annabi Shemaiya, da na Iddo maigani. Kullum yaƙi ne tsakanin Rehobowam da Yerobowam.