Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Sarakuna 11:43 - Littafi Mai Tsarki

43 Sulemanu ya rasu, aka binne shi a birnin Dawuda, wato Urushalima, ɗansa Rehobowam ya gaji sarautarsa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

43 Sa’an nan ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi a birnin Dawuda mahaifinsa. Sai Rehobowam ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Sarakuna 11:43
24 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Manassa ya mutu, aka binne shi a lambun gidansa a gonar Uzza. Ɗansa Amon ya gāji gadon sarautarsa.


Sa'an nan Dawuda ya rasu, aka binne shi a birnin Urushalima.


Sulemanu ya haifi Rehobowam, Rehobowam ya haifi Abiya, Abiya ya haifi Asa,


Salmon ya haifi Bo'aza (uwa tasa Rahab ce), Bo'aza ya haifi Obida (mahaifiyarsa Rut ce), Obida ya haifi Yesse,


Za a binne shi kamar jaki, Za a ja shi a yar a bayan ƙofofin Urushalima.”


Ahaz ya rasu, suka binne shi cikin birnin Urushalima, amma ba su kai shi hurumin sarakunan Isra'ila ba. Hezekiya ɗansa ya gāji gadon sarautarsa.


Azariya ya rasu, suka binne shi tare da kakanninsa a hurumin sarakuna, gama suka ce, “Shi kuturu ne.” Sai Yotam ɗansa ya gāji gadon sarautarsa.


Yana da shekara talatin da biyu, ya ci sarauta, ya yi shekara takwas yana mulki a Urushalima, ba wanda ya yi baƙin cikin mutuwarsa. Aka binne shi a birnin Dawuda, amma ba a kaburburan sarakuna ba.


waɗansu marasa amfani, 'yan iska, suka taru suka goyi bayansa, suka raina Rehobowam ɗan Sulemanu, saboda a lokacin shi yaro ne, ba shi da ƙarfin zuciya, bai iya tsayayya da su ba.


Sulemanu ya rasu aka binne shi tare da kakanninsa a birnin tsohonsa Dawuda, Rehobowam ɗansa shi ya gāje shi.


Waɗannan su ne zuriyar Sulemanu, daga Rehobowam, sai Abaija, da Asa, da Yehoshafat,


Aka binne shi a kabarinsa na gonar Uzza. Ɗansa Yosiya ya gāji sarautarsa.


Hezekiya kuwa ya rasu. Sai ɗansa, Manassa, ya gāji gadon sarautarsa.


Ahaz ya mutu, aka binne shi a makabartar kakanninsa a birnin Dawuda. Sai ɗansa, Hezekiya, ya gaji sarautarsa.


Ba'asha kuwa ya rasu, aka binne shi a Tirza. Sai Ila, ɗansa ya gāji sarautarsa.


Asa kuwa ya rasu, aka binne shi a Urushalima, Ɗansa Yehoshafat ya gāji sarautarsa.


Abaija ya rasu, suka binne shi a Urushalima. Ɗansa Asa ya gāji sarautarsa.


Rehobowam kuwa ya rasu, aka binne shi a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Na'ama, ita kuwa Ba'ammoniya ce. Ɗansa, Abaija ya gāji sarautar.


In ba haka ba, zai zama sa'ad da ka rasu za a ɗauka ni da ɗana, sulemanu, masu laifi ne.”


Ubangiji ya ce wa Musa, “Ga shi, za ka rasu ka tarar da kakanninka. Wannan jama'a kuwa za ta fara kaucewa daga hanya, su bi gumakan ƙasar da za su shiga, su zauna. Za su rabu da ni, su ta da alkawarina wanda na yi da su.


A Urushalima, Sulemanu ya yi shekara arba'in yana mulkin dukan Isra'ila.


Ahab ya rasu kamar kakanninsa. Ɗansa Ahaziya ya gāji sarautarsa.


Wa ya sani ko shi mai hikima ne, ko kuma wawa ne? Duk da haka shi zai mallaki dukan abin da na sha wahalar tanadinsa. Dukan aikin da na yi na hikima a wannan duniya aikin banza ne.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ