Sarautar ikonsa za ta yi ta ci gaba, Mulkinsa zai kasance da salama kullayaumin, Zai gāji sarki Dawuda, ya yi mulki a matsayinsa, Zai kafa mulkinsa a kan adalci da gaskiya, Tun daga yanzu har zuwa ƙarshen zamani. Ubangiji Mai Runduna ne ya yi niyyar aikata wannan duka.
Yusufu shi ma ya tashi daga birnin Nazarat, a ƙasar Galili, ya tafi ƙasar Yahudiya, ya je birnin Dawuda, da ake kira Baitalami (domin shi daga gidan Dawuda ne, na cikin zuriyarsa),
Na yage mulki daga gidan Dawuda na ba ka, duk da haka ba ka zama kamar bawana Dawuda ba, wanda ya kiyaye umarnaina, ya bi ni da zuciya ɗaya, yana yin abin da yake daidai a gare ni.
Da mutanen Isra'ila suka ga sarki ya ƙi jin roƙonsu, sai suka yi ihu, suna cewa, “A yi ƙasa da Dawuda da iyalinsa. Me suka taɓa yi mana? Mazajen Isra'ila, bari duka mu tafi gida! Mu bar Rehobowam ya lura da kansa!” Jama'ar Isra'ila fa suka tayar,
Idan za ka kasa kunne ga duk abin da na umarce ka, ka bi tafarkuna, ka aikata abin da yake daidai a gare ni, ka kiyaye dokokina da umarnaina kamar yadda bawana Dawuda ya yi, zan kasance tare da kai, zan sa gidanka ya kahu kamar yadda na sa gidan Dawuda ya kahu, zan ba ka Isra'ila.
Sulemanu kuwa ya nema ya kashe Yerobowam, amma Yerobowam ya tashi, ya tsere zuwa Masar, wurin Shishak Sarkin Masar, ya zauna a can har rasuwar Sulemanu.
Dukanmu mutuwa za mu yi, kamar ruwan da ya zube a ƙasa, wanda ba ya kwasuwa, haka za mu zama. Allah ba yakan ɗauke rai kurum ba, amma yakan shirya hanya domin wanda ya shuɗe ba zai ɓata daga gabansa ba.