Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Sarakuna 11:38 - Littafi Mai Tsarki

38 Idan za ka kasa kunne ga duk abin da na umarce ka, ka bi tafarkuna, ka aikata abin da yake daidai a gare ni, ka kiyaye dokokina da umarnaina kamar yadda bawana Dawuda ya yi, zan kasance tare da kai, zan sa gidanka ya kahu kamar yadda na sa gidan Dawuda ya kahu, zan ba ka Isra'ila.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

38 In ka aikata dukan abin da na umarce ka, ka yi tafiya a hanyoyina, ka kuma yi abin da yake daidai a idanuna ta wurin kiyaye farillaina da umarnaina, kamar yadda Dawuda bawana ya yi, zan kasance tare da kai. Zan gina maka masarauta mai dawwama kamar wadda na gina wa Dawuda, zan kuma ba da Isra’ila gare ka.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Sarakuna 11:38
20 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ba mutumin da zai yi tsayayya da kai dukan kwanakin ranka. Kamar yadda na kasance tare da Musa, haka zan kasance tare da kai, ba zan kunyatar da kai ba, ba kuwa zan yashe ka ba.


Ubangiji kansa zai bi da kai, ba zai kunyatar da kai ba, ba kuwa zai yashe ka ba. Kada ka ji tsoro, kada kuma ka karai.”


“Ubangiji Mai Runduna ya ce, ‘Idan ka yi tafiya a hanyata, ka kuma kiyaye umarnina, zan sa ka zama shugaban Haikalina, ka lura da shirayina, zan kuma sa ka sami damar zuwa wurin waɗannan da yake tsaye.


tun lokacin da na sa hakimai su shugabanci jama'ata Isra'ila. Zan rinjayi dukan maƙiyanka. Banda wannan kuma na yi alkawari zan ci dukan maƙiyanka, in mallakar da su ga zuriyarka.


“Idan ka yi biyayya da dokokina da umarnaina, to, zan cika maka alkawarin da na yi wa tsohonka Dawuda.


Idan za ka yi mini biyayya ka kuma kiyaye dokokina, da umarnaina kamar yadda tsohonka Dawuda ya yi, to, zan ba ka tsawon rai.”


Gidanka kuwa da mulkinka za su dawwama a gabana har abada. Gadon sarautarka kuma zai kahu har abada.’ ”


muddin kun yi biyayya da muryar Ubangiji Allahnku, kuna kiyaye wannan umarni da na umarce ku da shi yau.


Yanzu fa, in za ku yi biyayya da ni, ku kuma kiyaye maganata, za ku zama mutanena. Dukan duniya tawa ce, amma ku za ku zama zaɓaɓɓiyar jama'ata,


Allah kuma ya ba ungozoman nan zuriya domin sun ji tsoronsa.


Kada ku ci shi domin ku sami zaman lafiya, ku da zuriyarku a bayanku, gama za ku riƙa aikata abin da yake daidai a gaban Ubangiji.


Zan zaɓar wa kaina amintaccen firist wanda zai aikata abin da nake so ya yi, zan kuwa ba shi zuriya da ko yaushe za su yi aiki a gaban zaɓaɓɓen sarkina.


Zan sa ka yi mulki a kan duk abin da ranka yake bukata, za ka zama Sarkin Isra'ila.


Zan wahalar da zuriyar Dawuda, amma ba har abada ba.’ ”


sa'ad da Sulemanu ya tsufa sai suka janye zuciyarsa zuwa bin waɗansu gumaka, bai bi Ubangiji Allahnsa da zuciya ɗaya kamar yadda tsohonsa, Dawuda, ya yi ba.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ