Da dukan mutane suka ji, cewa Yerobowam ya komo, sai suka aika a kirawo shi ga taron jama'a. Suka naɗa shi Sarkin Isra'ila duka. Ba wanda ya bi gidan Dawuda, sai dai kabilar Yahuza.
Duk da haka ba zan karɓe sarauta duka daga hannunsa ba, amma zan bar shi ya yi mulki muddin ransa saboda bawana Dawuda, wanda na zaɓa, wanda ya kiyaye umarnaina da dokokina.