1 Sarakuna 10:21 - Littafi Mai Tsarki21 Dukan finjalai na sarki Sulemanu, da zinariya aka yi su, haka kuma finjalan da suke cikin ɗakin da aka gina da katakai daga Lebanon, ba a yi wani finjali da azurfa ba, domin ba a mai da azurfa kome ba a kwanakin Sulemanu. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202021 Dukan kwaf Solomon zinariya ne, kuma dukan kayayyakin gida a Fadan da ake kira Kurmin Lebanon, zinariya ce zalla. Babu wani abin da aka yi da azurfa, domin ba a ɗauki azurfa a bakin kome ba a zamanin Solomon. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |