1 Sarakuna 10:11 - Littafi Mai Tsarki11 Bayan wannan kuma jiragen ruwa na Hiram da suka kawo zinariya daga Ofir, sun kuma kawo itacen almug da yawa, da duwatsu masu daraja daga can. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202011 (Jiragen ruwan Hiram suka kawo zinariya daga Ofir. Daga can kuma suka kawo kaya masu yawa na katakon almug, da kuma duwatsu masu daraja. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Saboda haka sai ka aiko mini da mutum wanda ya gwanance a kan aiki da azurfa, da tagulla, da baƙin ƙarfe, da kuma shunayya, da garura, da shuɗɗan zare, da wanda kuma ya gwanance da aikin sassaƙa, domin ya yi aiki tare da gwanayen mutane da nake da su a Yahuza da Urushalima, waɗanda tsohona Dawuda ya kawo.