Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Sarakuna 10:10 - Littafi Mai Tsarki

10 Sa'an nan Sarauniyar Sheba ta ba sarki talanti ɗari da ashirin na zinariya, da kayan yaji mai yawan gaske, da duwatsu masu daraja. Ba a taɓa kawo kayan yaji da yawa kamar yadda Sarauniyar Sheba ta kawo wa sarki Sulemanu ba.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

10 Ta kuma ba sarki talenti 120 na zinariya, da kayan yaji masu yawa, da kuma duwatsu masu daraja. Ba a taɓa kawo kayan yaji da yawa haka kamar yadda sarauniyar Sheba ta ba wa Sarki Solomon ba.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Sarakuna 10:10
12 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ta iso Urushalima da 'yan rakiya da yawa, da raƙuma ɗauke da kayan yaji, da zinariya da yawa, da duwatsu masu daraja. Sa'ad da ta zo wurin Sulemanu, ta faɗa masa duk abin da yake a ranta.


Da suka shiga gidan kuwa, sai suka ga ɗan yaron, tare da uwa tasa Maryamu, suka fāɗi gabansa suka yi masa sujada. Sa'an nan suka kwance kayansu, suka miƙa masa gaisuwar zinariya, da lubban, da mur.


Ran sarki yă daɗe! Da ma a ba shi zinariya daga Arabiya, Da ma a yi masa addu'a dukan lokaci, Allah ya sa masa albarka kullum!


Sarakunan Esbanya da na tsibirai, Za su ba shi kyautai, Sarakunan Arabiya da na Habasha Za su kawo masa kyautai.


Hiram kuma ya aika wa Sulemanu da zinariya mai nauyin talanti ɗari da ashirin.


Ubangiji ya ce wa Musa, “Ɗauki kayan yaji masu ƙanshi, su stakte, da onika, da galbanum tare da lubban. Su zama daidai wa daida.


Mahaifinsu, Isra'ila ya ce musu, “In tilas haka zai zama, sai ku yi wannan, ku ɗiba daga cikin zaɓaɓɓu, mafiya kyau na albarkar ƙasar a cikin tayakanku, ku kai wa mutumin tsaraba, da ɗan man shafawa na ƙanshi da 'yar zuma, da kayan yaji, da ƙaro, da tsabar citta, da ɓaure.


yana tare da ɗaukakar Allah. Hasken birnin yana ƙyalƙyali kamar wani irin nadirin dutse mai daraja, kamar yasfa, garau kamar ƙarau.


In ka san abin da kake faɗa, kana da wani abu wanda ya fi zinariya da lu'ulu'ai tamani.


Daga Haikalinka a Urushalima, Sarakuna sukan kawo maka kyautai.


Na tara wa kaina azurfa, da zinariya, daga baitulmalin ƙasashen da nake mulki. Mawaƙa mata da maza suna raira mini waƙa, ina da dukan irin matan da kowane namiji zai so.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ