1 Sarakuna 1:9 - Littafi Mai Tsarki9 Adonija kuwa ya yi hadaya da tumaki, da bijimai, da turkakkun dabbobi kusa da Dutsen Zohelet, wato dutsen maciji, wanda yake gab da Enrogel. Ya gayyaci dukan 'yan'uwansa, 'ya'yan sarki, da fādawan da suke a Yahuza. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20209 Wata rana Adoniya ya tafi Dutsen Zohelet kusa da En Rogel, inda ya yi hadayar tumaki, da shanun noma, da shanun da ake kiwo a gida. Ya kuma gayyaci ’yan’uwansa, wato, sauran ’ya’yan Sarki Dawuda, tare da dukan dattawan sarki da suka fito daga Yahuda, အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |