1 Sarakuna 1:48 - Littafi Mai Tsarki48 Sa'an nan ya ce, ‘Yabo ya tabbata ga Ubangiji Allah na Isra'ila wanda ya sa ɗaya daga cikin zuriyata ya hau gadon sarautata yau, idona kuwa ya gani.’ ” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202048 ya ce, ‘Yabo ga Ubangiji, Allah na Isra’ila, wanda ya bar idanuna suka ga magāji a kan kujerar sarautata a yau.’ ” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Waɗannan Lawiyawa kuma, wato Yeshuwa, da Kadmiyel, da Bani, da Hashabnaiya, da Sherebiya, da Hodiya, da Shebaniya, da Fetahiya su ne suka yi kiran sujada, suka ce, “Ku miƙe tsaye, ku yabi Ubangiji Allahnku, Ku yabe shi har abada abadin. Bari kowa ya yabi maɗaukakin sunanka, ya Ubangijii, Ko da yake ba yabon da ɗan adam zai yi har ya isa.”