Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Sarakuna 1:47 - Littafi Mai Tsarki

47 Banda wannan kuma, fādawa sun tafi su kai caffa ga sarki Dawuda, suna cewa, ‘Allahnka ya sa Sulemanu ya yi suna fiye da kai, ya kuma fīfita gadon sarautarsa fiye da naka.’ Sai sarki ya sunkuyar da kansa a gadonsa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

47 Yanzu haka, fadawa sun zo suna wa ranka yă daɗe, Sarki Dawuda, sam barka, suna cewa, ‘Bari Allahnka yă sa sunan Solomon yă zama sananne fiye da naka, bari kuma sarautarsa tă fi taka girma!’ Sarki kuwa ya rusuna, ya yi sujada a kan gadonsa

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Sarakuna 1:47
9 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Kamar yadda Ubangiji ya kasance tare da ubangijina, sarki, haka kuma ya kasance tare da Sulemanu, ya fifita gadon sarautarsa fiye da na ubangijina, sarki Dawuda!”


Sai Yakubu ya ce, “Rantse mini.” Sai Yusufu ya rantse masa. Sa'an nan sai Isra'ila ya mai da kai bisa kan gadonsa.


Ta wurin bangaskiya Yakubu, sa'ad da yake bakin mutuwa, ya sa wa 'ya'yan Yusufu albarka dukkansu biyu, ya kuma yi sujada, yana sunkuye a kan sandarsa.


Suka ce, “Albarka ta tabbata ga Sarkin nan mai zuwa da sunan Ubangiji! Salama ta tabbata a Sama, ɗaukaka kuma ga Allah!”


domin su miƙa wa Allah na Sama sadaka mai daɗin ƙanshi, su kuma yi addu'a saboda sarki da 'ya'yansa.


Dawuda kuwa ya kira Gibeyonawa ya ce musu, “Me zan yi muku, da me zan yi kafara, domin ku sa wa mutanen Ubangiji albarka?”


sai ya aiki Adoniram ɗansa wurin sarki Dawuda don ya gaishe shi, ya kuma yaba masa saboda ya ci Hadadezer da yaƙi, gama Hadadezer yakan yi yaƙi da Toyi kullum. Adoniram kuwa ya kawo wa Dawuda kyautar kayan azurfa, da na zinariya, da na tagulla.


Kwashi garkunanku na tumaki da awaki, da na shanu, ku yi tafiyarku kamar yadda kuka ce, amma ku sa mini albarka.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ