Sai Sulemanu ya zauna a kan gādon sarauta na Ubangiji maimakon tsohonsa Dawuda. Ya yi nasara a cikin sarautar, Isra'ilawa dukansu suka yi masa biyayya.
Ka yi wa Dawuda muhimmin alkawari, Ba kuwa za ka ta da alkawarin ba. Ka ce, “Za naɗa ɗaya daga cikin 'ya'yanka maza yă zama sarki, Zai yi mulki a bayanka.
Zan kuma hamɓare gadon sarautan daula, in kuma karya ƙarfin daular al'umman. Zan kuma hallaka karusai da mahayansu. Sojojin dawakai kuma za su kashe junansu da takuba.
Ki tafi wurin sarki Dawuda, ki ce masa, ‘Ran sarki ya daɗe, ashe, ba ka rantse mini ba cewa, Sulemanu ɗana zai yi mulki bayanka, shi ne kuma zai hau gadon sarautarka? Me ya sa Adonija ya zama sarki?’