Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Sarakuna 1:25 - Littafi Mai Tsarki

25 Gama yau ɗin nan ya tafi ya miƙa hadaya da bijimai, da turkakkun dabbobi, da tumaki da yawa. Ya kuma gayyaci dukan 'ya'yan sarki, da Yowab shugaban sojoji, da Abiyata firist. Ga shi, suna ci suna sha tare da shi, suna cewa, ‘Ran sarki Adonija ya daɗe.’

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

25 Yau ya gangara, ya kuma miƙa hadayun shanu, da shanun da ake kiwo a gida, da tumaki masu yawa. Ya gayyaci dukan ’ya’yan sarki maza, da shugaban mayaƙa, da kuma Abiyatar firist. A yanzu haka suna ci, suna sha, tare da shi, suna cewa, ‘Ran Sarki Adoniya yă daɗe!’

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Sarakuna 1:25
19 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sama'ila ya ce wa dukan jama'a, “Kun gan shi? Shi ne wanda Ubangiji ya zaɓa, babu wani kamarsa a cikin dukan jama'a.” Jama'a duka kuwa suka yi sowa suka ce, “Ran sarki ya daɗe!”


Ya miƙa hadaya da bijimai, da turkakkun dabbobi, da tumaki da yawa. Ya kuma gayyaci dukan 'ya'yan sarki, da Abiyata firist, da Yowab shugaban sojoji, amma bai gayyaci Sulemanu ɗanka ba.


Adonija kuwa ya yi hadaya da tumaki, da bijimai, da turkakkun dabbobi kusa da Dutsen Zohelet, wato dutsen maciji, wanda yake gab da Enrogel. Ya gayyaci dukan 'yan'uwansa, 'ya'yan sarki, da fādawan da suke a Yahuza.


Suka ce, “Albarka ta tabbata ga Sarkin nan mai zuwa da sunan Ubangiji! Salama ta tabbata a Sama, ɗaukaka kuma ga Allah!”


Taron jama'a da suke tafiya a gabansa da kuma a bayansa, sai suka ɗauki sowa suna cewa, “Hosanna ga Ɗan Dawuda! Albarka ta tabbata ga mai zuwa da sunan Ubangiji! Hosanna ga Allah!”


Sai ya kawo ɗan sarkin, ya sa masa kambi, ya ba shi dokoki goma, aka yi shela aka ce shi ne sarki. Yehoyada da 'ya'yansa maza suka naɗa shi, suka ce, “Ran sarki ya daɗe!”


Kashegari sai suka miƙa wa Ubangiji hadayu, suka kuma miƙa hadayun ƙonawa ga Ubangiji, bijimai dubu ɗaya (1,000), da raguna dubu ɗaya (1,000), da 'yan raguna dubu ɗaya (1,000), da hadayunsu na sha, da hadayu masu yawa domin Isra'ila duka.


Yanzu ya Allahnmu, muna gode maka muna kuma yabon sunanka mai daraja.


Sa'an nan ya fito da ɗan sarki, ya sa kambin sarauta a kansa, ya kuma ba shi dokokin. Suka naɗa shi, suka zuba masa man naɗawa, sa'an nan suka yi tāfi suna cewa, “Ran sarki ya daɗe.”


a can Zadok firist, da annabi Natan za su zuba masa mai, ya zama sarkin Isra'ila, sa'an nan ku busa ƙaho, ku ce, ‘Ran sarki Sulemanu ya daɗe.’


Sa'ad da Hushai Ba'arkite, aminin Dawuda ya zo wurin Absalom, ya ce masa, “Ran sarki ya daɗe!”


Har wa yau ya sāke aiken waɗansu bayi, ya ce, ‘Ku gaya wa waɗanda aka gayyata, “Ga shi, na shisshirya abinci, an yanka shanuna da kiwatattun maruƙana, duk an shirya kome, ku zo bikin mana!” ’


Sa'an nan ya ce, “Ranka ya daɗe, ashe, ko ka sanar, cewa Adonija ne zai gaje ka?


A can ne Zadok, firist, ya ɗauki ƙahon mai wanda ya kawo daga alfarwa ta sujada, ya zuba wa Sulemanu. Sa'an nan suka busa ƙaho, dukan mutane kuwa suka ce, “Ran sarki Sulemanu ya daɗe.”


Ya amsa ya ce, “Kin sani dai sarauta tawa ce. Ni ne kuwa mutanen Isra'ila duka suka sa zuciya zan ci sarautar, amma al'amarin ya sāke, sai sarautar ta zama ta ƙanena, gama tasa ce bisa ga nufin Allah.


Sai kowane mutum a cikinsu ya yi maza ya tuɓe rigarsa, ya shimfiɗa a kan matakan, sa'an nan suka busa ƙaho, suna cewa, “Yehu ne sarki.”


Da ta duba, sai ta ga sarki a tsaye kusa da ginshiƙi bisa ga al'ada, shugabanni da masu busa kuwa suna tsaye kusa da sarki. Dukan mutanen ƙasar suna ta murna suna ta busa ƙaho. Sai Ataliya ta kece tufafinta, ta yi ihu, tana cewa, “Tawaye, tawaye!”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ