Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Sarakuna 1:16 - Littafi Mai Tsarki

16 Bat-sheba ta rusuna, ta gai da sarki. Sai sarki ya ce mata, “Me kike so?”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

16 Batsheba ta rusuna ta kuma durƙusa a gaban sarki. Sai sarki ya tambaye ta ya ce, “Me kike so?”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Sarakuna 1:16
10 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Da Abigail ta ga Dawuda, sai ta yi sauri ta sauka daga kan jakin, ta durƙusa gabansa har ƙasa.


Daga baya kuma Dawuda ya fita daga kogon, ya yi kira, ya ce, “Ya ubangijina, sarki.” Da Saul ya waiwaya, sai Dawuda ya rusuna.


Da yaron ya tafi, sai Dawuda ya tashi daga inda ya ɓuya kusa da tarin duwatsun, ya rusuna har sau uku. Sa'an nan suka sumbaci juna, suka yi kuka, amma Dawuda ya fi yi.


Sai Yesu ya tsaya, ya yi kiransu ya ce, “Me kuke so in yi muku?”


Sai ya ce mata, “Me kike bukata?” Ta ce masa, “Ka yi umarni waɗannan 'ya'yana biyu su zauna, ɗaya a damanka, ɗaya a hagunka, a mulkinka.”


A rana ta biyu, sa'ad da suke shan ruwan inabi, sai sarki ya sāke ce wa Esta, “Mece ce bukatarki, sarauniya Esta? Za a yi miki. Mene ne roƙonki? Za a ba ki, ko da rabin mulkina ne.”


Sai ta ce, “Ina da wani ɗan roƙo a gare ka, kada ka hana mini shi.” Sarki ya ce mata, “Ya tsohuwata, sai ki faɗi abin da kike so, gama ba zan hana miki ba.”


Aka faɗa wa sarki cewa, ga annabi Natan. Da ya zo gaban sarki, sai ya rusuna ya gaishe shi.


Bat-sheba kuwa ta tafi wurin sarki a ɗakinsa. Sarki dai ya tsufa ƙwarai, Abishag, yarinyar nan daga Shunem, tana yi masa hidima.


Ta ce masa, “Ranka ya daɗe, ka riga ka rantse mini da sunan Ubangiji Allahnka, ka ce, ‘Sulemanu ɗanki zai yi mulki bayana, shi ne zai hau gadon sarautata.’


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ