Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Sarakuna 1:1 - Littafi Mai Tsarki

1 Sarki Dawuda ya tsufa ƙwarai, don haka ko an rufe shi da abin rufa ba ya jin ɗumi.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

1 Sa’ad da Sarki Dawuda ya tsufa ya kuma ƙara shekaru, ba ya iya jin ɗumi ko an rufe shi da abin rufuwa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Sarakuna 1:1
13 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Tsawon kwanakin ranmu duka a ƙalla shekara ce saba'in, In kuwa muna da ƙarfi, shekara tamanin ne. Duk da haka iyakar abin da waɗannan shekaru Suke kawo mana, damuwa ce da wahala, Nan da nan sukan wuce, Tamu da ƙare.


Sa'ad da Dawuda ya tsufa, yana da shekaru da yawa, sai ya naɗa ɗansa Sulemanu ya zama Sarkin Isra'ila.


Dawuda ya ci sarauta yana da shekara talatin. Ya yi shekara arba'in yana sarauta.


Yanzu Ibrahim ya tsufa, ya kuwa kwana biyu. Ubangiji kuma ya sa wa Ibrahim albarka a cikin abu duka.


Ga shi kuwa, Ibrahim da Saratu sun tsufa, sun kwana biyu, gama Saratu ta daina al'adar mata.


Amma ba su da ɗa, don Alisabatu bakararriya ce, dukansu biyu kuma sun tsufa.


Sa'an nan ya gina wa Ubangiji bagade a wurin. Ya miƙa hadayun ƙonawa da na salama. Sa'an nan Ubangiji ya amsa masa addu'o'i saboda ƙasar. Aka kawar wa Isra'ila da annobar.


Saboda haka fādawansa suka ce masa, “Ranka ya daɗe bari mu nemo maka budurwa, wadda za ta zauna tare da kai, ta riƙa yin maka hidima, ta kwanta a ƙirjinka don ka riƙa jin ɗumi.”


Bat-sheba kuwa ta tafi wurin sarki a ɗakinsa. Sarki dai ya tsufa ƙwarai, Abishag, yarinyar nan daga Shunem, tana yi masa hidima.


Idan mutum biyu sun kwanta tare, za su ji ɗumin juna, amma ƙaƙa mutum ɗaya zai ji ɗumi?


Yanzu Joshuwa ya tsufa ƙwarai, sai Ubangiji ya ce masa, “Ka tsufa ƙwarai, ga shi, ƙasar da za ku mallaka ta ragu da yawa.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ