Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Samaʼila 9:25 - Littafi Mai Tsarki

25 Sa'ad da suka gangaro daga wurin yin sujadar zuwa cikin gari, sai aka shirya wa Saul gado a kan bene.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

25 Bayan suka gangaro daga tudu zuwa cikin gari, Sai Sama’ila ya yi magana da Shawulu a ɗakin samansa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Samaʼila 9:25
9 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Kashegari suna cikin tafiya, sun zo kusa da gari ke nan, sai Bitrus ya hau kan soro yin addu'a, wajen rana tsaka.


“Sa'ad da kuka gina sabon gida, sai ku ja masa rawani don kada ku jawo wa gidanku alhakin jini idan wani ya fāɗi daga bisa.


Sai suka tafi suka kawo rassan, suka yi wa kansu bukkoki a kan rufin sorayensu, da a dandalinsu, da cikin harabar Haikalin Allah, da a dandalin Ƙofar Ruwa, da a dandalin Ƙofar Ifraimu.


Wata rana da yamma Dawuda ya tashi daga shaƙatawa, yana yawo a kan rufin soron fādarsa, can ya hangi wata kyakkyawar mata tana wanka.


Abin da nake gaya muku a asirce, ku faɗa a sarari. Abin da kuma kuka ji a raɗe, ku yi shelarsa daga kan soraye.


Gidajen Urushalima da gidajen sarakunan Yahuza da dukan gidaje waɗanda a kan rufinsu aka ƙona wa rundunar sararin sama turare, aka zuba wa gumaka hadayu na sha, za su ƙazantu kamar Tofet.’ ”


Wanda yake soro, kada ya sauko garin ɗaukar wanda yake a gidansa.


Da suka kasa samun hanyar shigar da shi saboda taro, suka hau a kan soron, suka zura shi ta tsakanin rufin soron duk da shimfiɗarsa, suka ajiye shi a tsakiyar jama'a a gaban Yesu.


Ya kwanta, ya yi barci. Da asuba, Sama'ila ya kira Saul ya ce, “Tashi, in sallame ka.” Saul kuwa ya tashi, shi da Sama'ila suka fita waje zuwa kan titi.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ