Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Samaʼila 9:21 - Littafi Mai Tsarki

21 Saul ya ce, “Ni mutumin kabilar Biliyaminu ne, kabilar da ta fi ƙanƙanta a Isra'ila. Iyalina kuma su ne mafi ƙanƙanta a iyalan kabilar Biliyaminu. Me ya sa ka faɗa mini irin wannan magana?”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

21 Shawulu ya ce, “Ashe, ni ba mutumin Benyamin ba ne daga ƙaramar kabila ta Isra’ila? Dangina kuma ba shi ba ne mafi kakanni a cikin kabilar Benyamin ba? Yaya za ka faɗa mini irin wannan magana.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Samaʼila 9:21
13 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sama'ila ya ce, “Ko da yake kana ganin kanka kai ba wani abu ne ba, ashe, ba kai ne yanzu shugaban kabilan Isra'ila ba? Ubangiji ya sa ka zama Sarkin Isra'ila,


Ko da yake ni ne mafi ƙanƙantar tsarkaka duka, ni aka ba wannan alheri in yi wa al'ummai bishara a kan yalwar Almasihu marar ƙididdiguwa,


Duk wanda ya ɗaukaka kansa, za a ƙasƙantar da shi. Mai ƙasƙantar da kansa kuma, ɗaukaka shi za a yi.”


Ga Biliyaminu mafi ƙanƙanta Cikin kabilai, a kan gaba, Sa'an nan shugabannin Yahuza da ƙungiyarsu, Daga nan sai shugabannin Zabaluna da na Naftali suna biye da su.


Sa'ad da Ifraimu ta yi magana, mutane suka yi rawar jiki. An ɗaukaka ta cikin Isra'ila, Amma ta yi laifi ta wurin bauta gunkin nan Ba'al, Ta kuwa mutu.


Fādawan Saul kuwa suka faɗa wa Dawuda wannan magana. Sai Dawuda ya ce, “Zama surukin sarki ƙaramin abu ne a ganinku? Ga shi, ni talaka ne wanda ba sananne ba.”


Dawuda, ya ce wa Saul, “Wane ni ko iyalin mahaifina a cikin Isra'ila, har da zan zama surukin sarki?”


Amma waɗansu shashashan mutane suka ce, “Ƙaƙa wannan yaro zai iya cetonmu?” Suka raina shi, ba su kawo masa gaisuwa ba. Amma bai ce kome ba.


Sa'an nan Sama'ila ya shigar da Saul da baransa a babban ɗakin taruwa, ya sa su zauna gaba inda baƙi suke, wajen mutum talatin aka gayyata.


Kish mahaifin Saul, da Ner mahaifin Abner, 'ya'yan Abiyel ne.


Ka nuna ikonka, ya Allah, Ikon nan da ka nuna saboda mu.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ