Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Samaʼila 9:16 - Littafi Mai Tsarki

16 Ya ce masa, “Gobe war haka zan aiko maka da wani mutum daga kabilar Biliyaminu, sai ka zuba masa mai, ka keɓe shi sarki bisa jama'ata Isra'ila. Zai ceci jama'ata daga hannun Filistiyawa, gama na ga azabar da jama'ata suke sha, gama na ji kukansu.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

16 “Gobe war haka zan aiko maka da wani mutum daga ƙasar Benyamin. Ka keɓe shi shugaban mutanena Isra’ila. Shi zai cece mutanena daga hannun Filistiyawa. Na ga azabar mutanena gama kukansu ya hauro wurina.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Samaʼila 9:16
17 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sa'an nan Sama'ila ya ɗauki 'yar kwalabar mai, ya zuba wa Saul a kā, ya yi masa sumba, ya ce, “Ubangjiji ne ya keɓe ka, ya naɗa ka sarki a kan jama'arsa.


Duk da haka Ubangiji ya ji su sa'ad da suka yi kira gare shi, Ya kula da wahalarsu.


Ka kula da wahalata da azabata, Ka gafarta dukan zunubaina.


Sama'ila ya ce wa Saul, “Ubangiji ya aike ni in zuba maka man keɓewa don ka zama sarkin mutanensa, Isra'ila. Yanzu sai ka yi biyayya da maganar Ubangiji.


Ka gayyaci Yesse zuwa wurin hadayar, zan nuna maka abin da za ka yi. Za ka zuba wa wanda na nuna maka mai.”


Ubangiji ya ce wa Sama'ila, “Har yaushe za ka yi ta ɓacin rai saboda Saul? Ga shi kuwa, na ƙi shi da zama Sarkin Isra'ila. Ka sami man zaitun ka ɗauka. Zan aike ka zuwa wurin Yesse mutumin Baitalami, gama na zaɓi ɗaya daga cikin 'ya'yansa maza ya zama sarki.”


To, yanzu sai ku yarda ya sarauce ku, gama Ubangiji ya yi wa Dawuda alkawari ya ce, ‘Ta hannun bawana, Dawuda, zan ceci jama'ar Isra'ila daga hannun Filistiyawa, da na dukan abokan gābansu.’ ”


“Ka koma, ka faɗa wa Hezekiya sarkin jama'ata cewa, ‘Ni Ubangiji Allahn kakanka, Dawuda, na ji roƙonka, na kuma ga hawayenka, saboda haka zan warkar da kai, a rana ta uku kuwa za ka haura zuwa Haikalin Ubangiji.


Ka ji addu'ata, ya Ubangiji, Ka ji kukana na neman taimako!


Sai Hanamel ɗan kawuna ya zo wurina a gidan waƙafi, bisa ga faɗar Ubangiji, ya ce mini, “Ka sayi gonata wadda take a Anatot a ƙasar Biliyaminu, gama kai ne ka cancanta ka mallake ta, kai ne za ka fanshe ta, sai ka saye ta.” Sa'an nan na sani wannan maganar Ubangiji ce.


Sa'an nan Saul da mutanen da suke tare da shi suka taru, suka tafi su yi yaƙi. Sai suka tarar Filistiyawa sun ruɗe suna ta yaƙi da junansu. Aka yi babbar yamutsewa.


Haka Ubangiji ya ceci Isra'ilawa a ranan nan. Yaƙin kuwa ya kai har gaba da Bet-awen.


Kana iya yin shirye-shiryenka, amma Allah ne yake bi da kai cikin ayyukanka.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ