Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Samaʼila 9:13 - Littafi Mai Tsarki

13 Da shigarku garin, za ku same shi kafin ya tafi cin abinci a wurin yin sadakar, can kan tudu, gama jama'a ba za su ci ba, sai ya je ya sa albarka a sadakar, sa'an nan waɗanda aka gayyata su ci. Ku haura yanzu, za ku same shi nan da nan.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

13 Da zarar kun shiga garin, za ku same shi kafin yă tafi cin abinci a wurin yin sadakar, can kan tudu. Gama jama’a ba za su ci ba, sai ya kai can ya sa albarka a sadakar, sa’an nan waɗanda aka gayyata su ci. Ku haura da sauri, za ku same.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Samaʼila 9:13
12 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Yesu ya ɗauki gurasar, bayan ya yi godiya ga Allah kuma, sai ya rarraba wa waɗanda suke zazzaune. Haka kuma ya yi da kifin, gwargwadon abin da ya ishe su.


Domin duk abin da Allah ya halitta kyakkyawa ne, kada kuma a ƙi kome muddin an karɓe shi da godiya,


In na yi godiya ga Allah a kan abincina, saboda me za a zarge ni a kan abin da na ci da godiya ga Allah?


Akwai kuwa waɗansu ƙananan jirage daga Tibariya da suka iso kusa da wurin nan da taron suka ci gurasa bayan Ubangiji ya yi godiya.


Sa'ad da yake cin abinci tare da su, sai ya ɗauki gurasa, ya yi wa Allah godiya, ya gutsura, ya ba su.


Da ya ɗauki gurasa biyar ɗin da kifi biyun, sai ya ɗaga kai sama, ya yi wa Allah godiya, ya gutsuttsura gurasar, ya yi ta ba almajiran, suna kai wa jama'a, duk kuma ya raba musu kifin nan biyu.


Suna cikin cin abinci, sai Yesu ya ɗauki gurasa, ya yi godiya ga Allah, ya gutsuttsura, ya ba almajiran, ya ce, “Ungo, ku ci. Wannan jikina ne.”


Sa'an nan ya umarci taron su zazzauna a ɗanyar ciyawa. Da ya ɗauki gurasa biyar ɗin da kifi biyun, sai ya ɗaga kai sama, ya yi wa Allah godiya, ya gutsuttsura gurasar, ya yi ta ba almajiransa, almajiran kuma suna bai wa jama'a.


Da ya ɗauki gurasa biyar ɗin da kifi biyu, sai ya ɗaga kai sama, ya yi wa Allah godiya, ya gutsuttsura su, ya yi ta ba almajiran, suna kai wa jama'a.


Zan zaɓar wa kaina amintaccen firist wanda zai aikata abin da nake so ya yi, zan kuwa ba shi zuriya da ko yaushe za su yi aiki a gaban zaɓaɓɓen sarkina.


Suka kuwa haura zuwa cikin garin. Da shigarsu suka ga Sama'ila ya nufo wajen da suke, za shi wurin da ake yin sujadar.


Mutum metan waɗanda ya gayyata daga Urushalima suka tafi tare da shi da zuciya ɗaya ba tare da sanin kome ba.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ