Goliyat ya ta da murya da ƙarfi, ya yi kira ga rundunar Isra'ila, ya ce, “Don me kuka fito ku jā dāgar yaƙi? Ai, ni Bafiliste ne, ku kuwa barorin Saul! Ku zaɓi mutum guda daga cikinku ya gangaro nan wurina.
Shi ne kuwa Ibrahim ya ba shi ushirin kome. Da farko dai, kamar yadda ma'anar sunansa take, shi sarkin adalci ne, sa'an nan kuma Sarkin Urushalima ne, wato, sarkin salama.