1 Samaʼila 8:12 - Littafi Mai Tsarki12 Waɗansu kuma zai sa su zama shugabannin mutum dubu dubu da na hamsin hamsin. 'Ya'yanku ne za su riƙa yi masa noma da girbi, su ƙera masa kayayyakin yaƙi da na karusansa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202012 Zai sa waɗansu su zama shugabannin mutum dubu-dubu da kuma na hamsin-hamsin. Waɗansu za su yi masa noma da girbi. Waɗansu za su ƙera masa makaman yaƙi da kayayyaki don keken yaƙinsa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sai ya ce wa fādawan da suke tsaye kewaye da shi, “Ku ji, ya ku mutanen Biliyaminu, ɗan Yesse zai ba kowannenku gonaki, da gonakin inabi ne? Zai maishe ku shugabanni na dubu dubu, da na ɗari ɗari, har da dukanku kuka yi mini maƙarƙashiya? Ba wanda ya sanar da ni sa'ad da ɗana ya haɗa kai da ɗan Yesse? Ba wanda ya damu saboda da ni, balle a faɗa mini yadda ɗana ya kuta barana ya tayar mini, yana fakona, kamar yadda yake a yau?”