1 Samaʼila 8:11 - Littafi Mai Tsarki11 Ya ce musu, “Ga irin halin sarkin da zai sarauce ku, zai sa 'ya'yanku maza su zama sojojinsa, waɗansunsu za su yi aiki da karusan yaƙinsa, waɗansu su zama mahayan dawakansa, da masu kai hari musamman. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202011 Ya ce musu, “Ga abin da sarkin da zai yi mulkinku zai yi. Zai kwashe ’ya’yanku yă sa su yi aiki da kekunan yaƙi da dawakansa, waɗansu za su riƙa gudu a gaban keken yaƙinsa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sai ya ce wa fādawan da suke tsaye kewaye da shi, “Ku ji, ya ku mutanen Biliyaminu, ɗan Yesse zai ba kowannenku gonaki, da gonakin inabi ne? Zai maishe ku shugabanni na dubu dubu, da na ɗari ɗari, har da dukanku kuka yi mini maƙarƙashiya? Ba wanda ya sanar da ni sa'ad da ɗana ya haɗa kai da ɗan Yesse? Ba wanda ya damu saboda da ni, balle a faɗa mini yadda ɗana ya kuta barana ya tayar mini, yana fakona, kamar yadda yake a yau?”