sai na ba ɗan'uwana, Hanani, da Hananiya, shugaban kagara, aikin riƙon Urushalima. Shi Hananiya mai aminci ne, mai tsoron Allah, fiye da sauran mutane.
Yana da 'ya'ya maza guda talatin, waɗanda suke hawan jakai talatin. Suna kuma da birane talatin a ƙasar Gileyad, waɗanda har yanzu ake kira biranen alfarwai. Ana kiran biranen Hawwot-Yayir, wato na Yayir.
Yanzu ga sarki a gabanku, 'ya'yana maza kuma suna tare da ku. Ni na tsufa, na yi furfura, amma na yi ta kai da kawowa a cikinku tun ina yaro har zuwa yau.