Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Samaʼila 7:4 - Littafi Mai Tsarki

4 Isra'ilawa kuwa suka rabu da gumakan Ba'al da Ashtarot, suka bauta wa Ubangiji shi kaɗai.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

4 Sai Isra’ilawa suka rabu da gumakan Ba’al da Ashtarot suka bauta wa Ubangiji kaɗai.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Samaʼila 7:4
11 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ya mutanen Ifraimu, me zan yi da gumaka? Ni ne wanda yake amsa muku, mai lura da ku kuma. Ni kamar itacen fir ne mai ganyaye kore shar. Daga gare ni, kuke samun 'ya'ya.”


Assuriya ba za ta cece mu ba, Ba kuwa za mu hau dawakai ba. Ba za mu kuma ƙara ce da aikin hannuwanmu, ‘Kai ne Allahnmu,’ ba. A wurinka ne maraya yakan sami jinƙai.”


Domin Sulemanu ya rabu da ni, ya bauta wa Ashtoret, gunkiyar Sidoniyawa, da Kemosh, gunkin Mowab, da Milkom, gunkin Ammonawa. Bai yi tafiya a cikin tafarkuna ba, bai yi abin da yake daidai a gare ni ba, bai kiyaye dokokina, da ka'idodina kamar yadda Dawuda, tsohonsa, ya yi ba.


Suka bar yi wa Ubangiji sujada suka bauta wa gumakan nan, wato Ba'al da Ashtarot.


Jama'ar Isra'ila kuwa suka yi wa Ubangiji zunubi, wato suka bauta wa gunkin nan mai suna Ba'al.


Sa'an nan Sama'ila ya ce wa mutanen Isra'ila, “Idan da zuciya ɗaya kuke komowa wurin Ubangiji, to, sai ku rabu da baƙin alloli, da gumakan nan Ashtarot. Ku sa zuciyarku ga bin Ubangiji, ku bauta masa shi kaɗai, shi kuwa zai cece ku daga hannun Filistiyawa.”


Sama'ila kuma ya ce, “Ku tattara dukan Isra'ilawa a Mizfa, ni kuwa zan yi addu'a ga Ubangiji dominku.”


Idan sun komo gare ka da zuciya ɗaya, da dukan ransu a ƙasar abokan gabansu waɗanda suka kai su bauta, suka yi addu'a gare ka, suna fuskantar ƙasarsu wadda ka ba kakanninsu, da birnin da ka zaɓa, da Haikalin da na gina saboda sunanka,


Gama Sulemanu ya bi Ashtoret ta Sidoniyawa, da Milkom, wato gunkin Ammonawa.


Yosiya ya kuma rushe bagaden da yake a Betel, wanda Yerobowam ɗan Nebat ya gina, wanda ya sa mutanen Isra'ila su yi zunubi, tare da tudun, ya farfashe duwatsun, ya niƙe su, sun zama gari, ya kuma ƙone Ashtoret.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ