Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Samaʼila 7:10 - Littafi Mai Tsarki

10 A sa'ad da Sama'ila yake miƙa hadaya ta ƙonawa, Filistiyawa suka matso don su yi yaƙi da Isra'ilawa, sai Ubangiji ya buge wa Filistiyawa tsawa mai ƙarfi daga sama, suka kuwa ruɗe suka juya a guje.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

10 Lokacin da Sama’ila yana miƙa hadaya ta ƙonawa, Filistiyawa suka matso kusa don su yi yaƙi da Isra’ila. A ranar Ubangiji ya sa babban tsawa ya ruɗar da Filistiyawa har suka gudu a gaban Isra’ilawa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Samaʼila 7:10
21 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Za a hallakar da maƙiyan Ubangiji, Zai yi musu tsawa daga Sama. Ubangiji zai hukunta dukan duniya, Zai ba sarkinsa iko, Zai sa zaɓaɓɓen sarkinsa ya zama mai nasara.”


Yanzu dai rani ne, ko ba haka ba? Zan roƙi Ubangiji ya aiko da tsawa da ruwan sama, da haka za ku sani, ku kuma ga babbar muguntar da kuka yi wa Ubangiji da kuka roƙa a yi muku sarki.”


Daga sama, taurari suka yi yaƙi, Suna gilmawa a sararin sama Suka yi yaƙi da Sisera.


Ubangiji kuwa ya sa suka gigice a gaban Isra'ilawa. Isra'ilawa suka kashe su da yawa a Gibeyon, suka runtume su ta hanyar haurawa zuwa Bet-horon. Suka yi ta karkashe su har zuwa Azeka da Makkeda.


Sa'an nan ya ce, “Wannan ita ce maganar Ubangiji zuwa ga Zarubabel cewa, ‘Ba da ƙarfi, ko iko ba, amma da Ruhuna,’ in ji Ubangiji Mai Runduna.


Sa'ad da Isra'ilawa suka zaɓi baƙin alloli, Sai ga yaƙi a ƙasar. Ba a ga garkuwa ko mashi A wurin mutum dubu arba'in na Isra'ila ba.


Ubangiji kuwa ya sa Barak ya yi kaca-kaca da Sisera, da karusansa duka, da rundunar mayaƙansa duka da takobi. Sisera kuwa ya sauka daga karusarsa, ya gudu da ƙafa.


Isra'ilawa suka fito daga Mizfa suka runtumi Filistiyawa, suka yi ta karkashe su har zuwa kwarin Bet-kar.


Dukan Filistiyawan da suke a filin suka ji tsoro, da mahara da sauran sojoji suka yi rawar jiki, ƙasa ta girgiza, aka yi babbar gigicewa.


An ji muryar Ubangiji a kan tekuna, Allah Maɗaukaki ya yi tsawa, Tsawar muryarsa kuwa ta yi amsa kuwa a bisa teku.


An ji muryar Ubangiji A dukan ikonsa da zatinsa!


“Ubangiji zai sa ku fatattaki abokan gābanku a gabanku waɗanda suke tasar muku. Ta hanya guda za su auka muku, amma ta hanyoyi bakwai za su gudu daga gabanku.


Kashiyar teku ta bayyana, Tussan duniya sun bayyana, Sa'ad da ka tsauta wa magabtana, ya Ubangiji, Sa'ad da kuma ka yi musu tsawa da fushi.


Ya tura abokan gābansa baya, Da mummunar kora mai bankunya Da ba za su sāke tashi ba.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ