Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Samaʼila 6:9 - Littafi Mai Tsarki

9 Ku zuba ido, ku gani, idan ya kama hanya zuwa Bet-shemesh, to, shi ne ya kawo mana wannan babbar masifa, amma idan ba haka ba, za mu sani ba shi ne ya buge mu ba, tsautsayi ne kawai.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

9 Amma ku zuba ido ku ga in ya haura zuwa yankinsa, zuwa Bet-Shemesh, to, Ubangiji ne ya kawo mana babban masifar a kanmu. Amma in bai bi ta nan ba, za mu san cewa ba shi ne ya buge mu ba, tsautsayi ne kawai.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Samaʼila 6:9
13 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ta kuma kewaye kudancin Ba'ala zuwa Dutsen Seyir. Ta zarce zuwa arewacin kafaɗar Dutsen Yeyarim, wato Kesalon. Daga nan ta gangara zuwa Bet-shemesh, ta kuma wuce zuwa Timna.


Daga nan ya zamana wani firist ya biyo ta wannan hanya. Da ya gan shi sai ya zaga ta ɗaya gefen, ya wuce abinsa.


Na gane wani abu kuma, ashe, a duniyan nan ba kullum maguji ne yake cin tsere ba, ba kullum jarumi ne yake cin nasara ba. Ba kullum mai hikima ne da abinci ba, ba kullum mai basira ne yake da wadata ba, ba kullum gwani ne yake samun tagomashi ba. Amma sa'a, da tsautsayi, sukan sami kowannensu.


Mutumin kuwa ya amsa ya ce, “Ya zama fa ina kan dutsen Gilbowa, sai ga Saul ya jingina a māshinsa. Karusai da mahayan dawakan abokan gāba sun rutsa shi.


Sai firistocin da bokayen suka ce, “Idan za ku komar da akwatin alkawarin Allah na Isra'ila, dole ku aika da kyauta tare da shi domin zunubinku. Ba dama a komar da akwatin alkawarin hannu wofi. Ta haka za ku sami lafiya, za ku kuma san dalilin da ya sa ya yi ta hukunta ku.”


da Ayin tare da wuraren kiwo nata, da Yutta tare da wuraren kiwo nata, da Bet-shemesh tare da wuraren kiwo nata. Birane tara ke nan daga cikin kabilun nan biyu.


Zai yiwu mutane su rasa firgita, Idan aka busa ƙahon yaƙi a birni? Zai yiwu wata babbar masifa ta auko wa birni Ba da yardar Ubangiji ba?


Maƙiyanka ba su san za ka hukunta su ba. Ya Ubangiji, ka kunyatar da su, ka sa su sha wahala, Wato su sha wahalar hukuncin da ka shirya. Ka nuna musu yawan ƙaunar da kake yi wa jama'arka.


Suka yi yadda aka faɗa musu, suka sami shanun tatsa biyu, suka ɗaura musu karkiyar keken. Suka tsare 'yan maruƙansu a gida.


Shanun kuwa suka kama hanya sosai wadda ta nufi wajen Bet-shemesh, suna tafe, suna ta kuka, ba su kauce zuwa dama ko hagu ba, sarakunan Filistiyawa suna biye da su, har zuwa iyakar Bet-shemesh.


Da Fir'auna ya ga an kawar masa da kwaɗin, sai ya taurare zuciyarsa, ya ƙi jinsu kamar yadda Ubangiji ya riga ya faɗa.


Sarkin Isra'ila kuwa ya haura, da shi da Amaziya Sarkin Yahuza, suka gabza da juna fuska da fuska a Bet-shemesh, wadda take a ƙasar Yahuza.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ