Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Samaʼila 6:4 - Littafi Mai Tsarki

4 Suka ce, “Wace irin hadaya za mu bayar?” Firistocin suka ce, “Sai ku yi marurai biyar na zinariya da ɓeraye biyar na zinariya bisa ga yawan sarakunan Filistiyawa, gama annoba iri ɗaya ce ta same ku da sarakunanku.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

4 Filistiyawa suka ce, “Wace irin hadaya don laifi za mu aika masa?” Suka ce, “Marurai biyar na zinariya da ɓeraye biyar na zinariya bisa ga yawan sarakunan Filistiyawa. Saboda annoba iri ɗaya ce ta buga ku da shugabanninku.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Samaʼila 6:4
10 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Al'umman da suka ragu a ƙasar su ne, birane biyar na Filistiyawa, da dukan Kan'aniyawa, da Sidoniyawa, da Hiwiyawa da suke zaune a Dutsen Lebanon, tun daga Dutsen Ba'alharmon har zuwa mashigin Hamat,


daga Shihor da yake gabas da Masar zuwa iyakar Ekron a wajen arewa. Wannan ƙasa ta Kan'aniyawa ce. Akwai ƙasar sarakuna biyar na Filistiyawa da yake a Gaza, da Ashdod, da Ashkelon, da Gat, da Ekron, da ƙasar Awwiyawa,


Amma da suka kai shi can sai Ubangiji ya hukunta birnin, ya gigita su, ya yi musu azaba da marurai, yara da manya.


Ubangiji kuwa ya hukunta mutanen Ashdod ƙwarai da gaske, ya kuma razanar da su, ya azabtar da su da marurai, su da na kewaye da su.


Ku yi siffofin marurai da na ɓeraye waɗanda suka lalatar da ƙasar, ku ba da girma ga Allah na Isra'ila, watakila zai ɗauke hukuncinsa a kanku, da allolinku, da ƙasarku.


Marurai sun fito wa mutanen da ba su mutu ba, mutane suka yi kuka domin allolinsu su cece su.


Isra'ilawa kuwa suka yi yadda Musa ya faɗa musu, suka roƙi Masarawa kayan adonsu na azurfa da na zinariya, da kuma tufafi.


Sa'an nan ku sa akwatin alkawarin Ubangiji a keken shanun, ku kuma sa siffofin maruran da na ɓerayen a cikin wani akwati ku ajiye a gefen akwatin alkawarin. Ku aika da waɗannan abubuwa tare da shi don yin hadaya ta laifi. Sa'an nan ku sa shi a hanya, a bar shi, ya tafi.


Sa'an nan Ruhun Ubangiji ya sauko a kansa da iko, ya gangara zuwa Ashkelon. Ya kashe mutum talatin a can, ya kwashe ganima, ya ba waɗanda suka faɗa masa amsar ka-cici-ka-cicin riguna. Ya koma gida a husace saboda abin da ya faru.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ