Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Samaʼila 5:9 - Littafi Mai Tsarki

9 Amma da suka kai shi can sai Ubangiji ya hukunta birnin, ya gigita su, ya yi musu azaba da marurai, yara da manya.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

9 Amma bayan sun kai shi can, sai hannun Ubangiji ya yi gāba da birnin, aka jefa shi cikin wani mawuyacin hali. Ya buga mutanen birnin da marurai, babba da yaro.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Samaʼila 5:9
11 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ubangiji kuwa ya hukunta mutanen Ashdod ƙwarai da gaske, ya kuma razanar da su, ya azabtar da su da marurai, su da na kewaye da su.


Ta haka aka ci Filistiyawa. Daga nan ba su ƙara shiga yankin ƙasar Isra'ilawa ba, gama Ubangiji ya yi gāba da Filistiyawa a dukan zamanin Sama'ila.


Hakika kuwa ikon Ubangiji ya buge su har suka hallaka ƙaƙaf.


Amma idan kun ƙi yin biyayya da maganar Ubangiji, kuka kuma karya umarnin Ubangiji, to, Ubangiji zai yi gāba da ku da sarkinku.


Ya tura abokan gābansa baya, Da mummunar kora mai bankunya Da ba za su sāke tashi ba.


Zai zama kamar wanda ya tsere wa zaki Ya fāɗa a bakin beyar! Ko kuwa kamar wanda ya komo gida, Ya dāfa bango, maciji ya sare shi.


Suka sa akwatin alkawarin Ubangiji a keken, da akwatin siffofin ɓerayen zinariya da siffofin maruran.


Suka kuma aika a kirawo sarakunan Filistiyawa, suka ce, “Ku aika da akwatin alkawarin Allah na Isra'ila zuwa inda ya fito don kada ya kashe mu duk da iyalinmu.” Dukan birnin ya gigita ƙwarai, gama Ubangiji yana hukunta su da tsanani.


Sai suka kai akwatin alkawarin Allah zuwa Ekron. Amma da aka kai shi Ekron, sai mutanen Ekron suka fashe da kuka, suka ce, “Sun kawo mana akwatin alkawarin Allah na Isra'ila don ya kashe dukanmu.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ