Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Samaʼila 5:8 - Littafi Mai Tsarki

8 Sai suka aika, aka kirawo dukan sarakunan Filistiyawa, su biyar, suka ce musu, “Me za mu yi da akwatin alkawarin Allah na Isra'ila?” Suka ce, “Sai a kai shi Gat.” Su kuwa suka kai shi can.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

8 Saboda haka suka kira duka shugabannin Filistiyawa suka tambaye su, suka ce, “Me za mu da akwatin alkawarin Allahn Isra’ila?” Sai suka amsa suka ce, “A ɗauki akwatin alkawarin Allah na Isra’ila a kai shi Gat.” Sai suka ɗauki akwatin alkawarin Allah na Isra’ila.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Samaʼila 5:8
11 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

A ran nan zan sa Urushalima ta zama dutse mai nauyi ga dukan al'ummai. Duk wanda ya ɗaga ta zai ji wa kansa mugun rauni. Dukan al'umman duniya za su taru su kewaye ta.


Ku je ku duba a birnin Kalne. Sa'an nan ku zarce zuwa babban birnin Hamat, Har zuwa birnin Gat ta Filistiyawa. Sun fi mulkin Yahuza da Isra'ila ne? Ko kuwa, yankin ƙasarsu ya fi naku?


Akwai wani jarumi, sunansa Goliyat, ya fito daga sansanin Filistiyawa. Tsayinsa kamu shida da rabi.


Suka kuma aika a kirawo sarakunan Filistiyawa, suka ce, “Ku aika da akwatin alkawarin Allah na Isra'ila zuwa inda ya fito don kada ya kashe mu duk da iyalinmu.” Dukan birnin ya gigita ƙwarai, gama Ubangiji yana hukunta su da tsanani.


Da mutanen Ashdod suka ga yadda abin yake, sai suka ce, “Kada a bar akwatin alkawarin Allah na Isra'ila tare da mu, gama ya tsananta mana, mu da Dagon, allahnmu.”


Akish kuwa ya kira Dawuda, ya ce masa, “Kai amintacce ne a ganina, daidai ne kuma ka tafi yaƙi tare da ni, gama ban same ka da wani laifi ba tun daga ranar zuwanka wurina har yau, duk da haka sarakunan ba su amince da kai ba.


daga Shihor da yake gabas da Masar zuwa iyakar Ekron a wajen arewa. Wannan ƙasa ta Kan'aniyawa ce. Akwai ƙasar sarakuna biyar na Filistiyawa da yake a Gaza, da Ashdod, da Ashkelon, da Gat, da Ekron, da ƙasar Awwiyawa,


Iyakar kuma ta biya wajen kafaɗar tudun, arewa da Ekron, sa'an nan ta karkata zuwa Shikkeron, ta wuce zuwa Dutsen Ba'ala, ta tafi zuwa Yabneyel, sa'an nan ta gangara a teku.


Filistiyawa suka kirawo firistocinsu da bokayensu, suka ce, “Me za mu yi da akwatin alkawarin Ubangiji? Ku sanar da mu yadda za mu komar da shi inda ya fito.”


Mutanen Isra'ila da na Yahuza suka tashi suka runtumi Filistiyawa, suna ihu, har zuwa Gat da ƙofofin Ekron. Filistiyawan da aka yi wa rauni suka yi ta faɗuwa a hanya tun daga Shayarim, har zuwa Gat da Ekron.


da Zabad, da Shutela, da Ezer, da Eleyad waɗanda mutanen Gat, haifaffun ƙasar, suka kashe sa'ad da suka kai hari don su kwashe dabbobinsu.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ