Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Samaʼila 5:4 - Littafi Mai Tsarki

4 Kashegari da safe kuma da suka tashi, sai suka ga Dagon ya faɗi rubda ciki a gaban akwatin alkawarin Ubangiji. Kan Dagon da hannuwansa a gutsure, suna nan a dokin ƙofa. Gangar jikin ce ta ragu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

4 Amma kashegari kuma da safe suka farka sai ga Dagon ya fāɗi a ƙasa a gaban akwatin alkawarin Ubangiji! Kansa ya fashe, hannuwansa kuma sun kakkarye sun zube a madogarar ƙofa; jikinsa ne kaɗai ya rage.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Samaʼila 5:4
11 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Za a farfashe dukan siffofinta na zubi, Za a ƙaƙƙone dukiyarta da wuta, Zan lalatar da gumakanta duka, Gama ta wurin karuwanci ta samo su, Ga karuwanci kuma za su koma.”


“Ku ba da labari ga sauran al'umma, ku yi shela, Ku ta da tuta, ku yi shela, Kada ku ɓuya, amma ku ce, ‘An ci Babila da yaƙi, An kunyatar da Bel, An kunyatar da siffofinta, Merodak ya rushe, Gumakanta kuma sun ragargaje!’


Haka za ku faɗa musu, “Gumakan da ba su yi sammai da duniya ba, za su lalace a duniya da a ƙarƙashin sammai.”


Zai kwashe gumakansu ganima, da siffofinsu na zubi, ya kai Masar, tare da tasoshinsu na azurfa da na zinariya masu daraja. Zai yi shekaru bai kai wa sarkin arewa yaƙi ba.


Ba za a gafarta zunuban Isra'ila ba, sai an niƙe duwatsun bagadan arna su zama kamar alli, har kuma ba sauran keɓaɓɓun ginshiƙai ko bagadan ƙona turare.


Ku yi siffofin marurai da na ɓeraye waɗanda suka lalatar da ƙasar, ku ba da girma ga Allah na Isra'ila, watakila zai ɗauke hukuncinsa a kanku, da allolinku, da ƙasarku.


Mutum wanda bai isa samun azurfa ko zinariya ba, Yakan zaɓi itacen da ba zai ruɓe ba. Yana neman gwanin sassaƙa Domin ya yi masa siffa wadda ba za ta fāɗi ba.


Kowane mutum dakiki ne, marar ilimi, Kowane maƙerin zinariya zai sha kunya saboda gumakansa, Gama siffofinsa ƙarya ne, Ba numfashi a cikinsu.


Su ba kome ba ne, aikin ruɗami ne, A lokacin da za a hukunta su za su lalace.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ