Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Samaʼila 4:19 - Littafi Mai Tsarki

19 Surukar Eli, matar Finehas, tana da juna biyu, ta kusa haihuwa. Sa'ad da ta ji labari an ƙwace akwatin alkawarin Allah, surukinta kuma da mijinta sun rasu, sai ta kama naƙuda farat ɗaya, ta haihu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

19 Matar Finehas, ɗansa tana da ciki a lokacin ta kuma kusa haihuwa. Sa’ad da ta ji labari cewa an ƙwace akwatin alkawarin Allah, ta kuma labarin surukinta da mijinta sun mutu, sai ta shiga naƙuda, ta kuma haihu. Amma naƙuda ta sha ƙarfinta.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Samaʼila 4:19
7 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Da aka ambaci akwatin alkawari, sai Eli ya tuntsura da baya daga inda yake zaune a bakin ƙofar gari, wuyansa kuwa ya karye, ya mutu, gama shi tsoho ne, mai ƙiba. Ya shekara arba'in yana shugabancin Isra'ila.


Tana bakin mutuwa, matan kuwa da take taimakonta suka ce mata, “Ki yi ƙarfin hali, gama kin haifi ɗa namiji.” Amma ba ta amsa ba, ba ta kuma kula ba.


Ga matar kuwa ya ce, “Zan tsananta naƙudarki ainun, da azaba za ki haifi 'ya'ya, duk da haka muradinki zai koma ga mijinki, zai kuwa mallake ki.”


Sa'ad da take cikin naƙudarta, sai ungozoma ta ce mata, “Kada ki ji tsoro, gama yanzu kin sami wani ɗa.”


A lokacin nan Abaija ɗan Yerobowam ya kwanta ciwo.


Aka karkashe firistoci da takuba, Matansu ba su yi makoki dominsu ba.


Saboda haka zan mai da wannan Haikali kamar Shilo, in mai da wannan birni ya zama abin la'ana ga dukan al'umman duniya.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ