Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Samaʼila 31:12 - Littafi Mai Tsarki

12 sai dukan jarumawa suka tashi, suka yi tafiya dukan dare. Suka ɗauko gawar Saul da gawawwakin 'ya'yansa daga kan garun Bet-sheyan. Da suka zo Yabesh sai suka ƙone su a can.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

12 Sai dukan jarumawansu suka tashi cikin dare suka tafi Bet-Shan suka saukar da gawar Shawulu da na ’ya’yansa daga kan katangan Bet-Shan suka tafi Yabesh inda suka ƙone su.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Samaʼila 31:12
6 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Aka binne shi a kabarin da shi da kansa ya haƙa a birnin Dawuda. Aka sa shi a makara wadda aka cika da kayan ƙanshi da na turare yadda gwanayen aikin turare suka shirya, suka hura babbar wuta don su darajanta shi.


Za ka mutu da salama. Kamar yadda aka ƙona wa sarakuna marigayanka turare, haka kai ma mutane za su ƙona maka turare, za su yi makoki dominka suna cewa, ‘Kaito, sarki ya rasu.’ Ni Ubangiji na faɗa.”


Sa'ad da dangin mamacin ya shiga don ya fitar da gawar, ya ƙone, sai ya yi kira ga ko wane ne da yake ɓoye a gidan, ya ce, “Ko akwai wani kuma a nan?” Sai a amsa, “A'a.” Zai ce, “Kul! Kada a ambaci sunan Ubangiji.”


Suka ajiye makaman Saul cikin haikalin gumakan nan Ashtarot. Suka ɗaure gawarsa a kan garun Bet-sheyan.


sai dukan ƙarfafan mutanensu suka tafi suka ɗauki gawar Saul, da gawawwakin 'ya'yansa, suka kawo a Yabesh suka binne ƙasusuwansu a ƙarƙashin itacen oak cikin Yabesh. Suka yi azumi har kwana bakwai.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ