Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Samaʼila 30:8 - Littafi Mai Tsarki

8 Sai Dawuda ya yi tambaya ga Ubangiji ya ce, “In bi sawun 'yan harin nan? Zan ci musu?” Ya ce masa, “Bi su, gama za ka ci musu, ka ƙwato abin da suka kwashe.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

8 Dawuda kuwa ya nemi nufin Ubangiji ya ce, “In bi bayan ’yan harin nan? Zan ci musu?” Ubangiji ya ce, “Bi su, gama za ka ci musu, ka ƙwato abin da suka kwashe.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Samaʼila 30:8
21 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Dawuda ya ƙwato dukan abin da Amalekawa suka kwashe, har da matansa biyu.


Sai Dawuda ya yi roƙo ga Ubangiji, ya ce, “Ko in tafi in fāɗa wa Filistiyawa da yaƙi?” Ubangiji kuwa ya ce wa Dawuda, “Tafi, ka yi yaƙi da Filistiyawa, ka ceci mutanen Kaila.”


Dawuda kuwa ya yi roƙo ga Ubangiji, ya ce, “Ko in tafi in yi yaƙi da Filistiyawa? Za ka bashe su a hannuna?” Ubangiji kuwa ya ce masa, “Ka haura, gama hakika, zan ba da Filistiyawa a hannunka.”


Dawuda ya kuma roƙi Ubangiji. Ubangiji kuwa ya ce masa, “Kada ka haura zuwa wurinsu gaba da gaba, amma ka bi ta bayansu, ka ɓullo musu daura da itatuwan doka.


Dawuda kuma ya sāke roƙon Ubangiji. Sai Ubangiji ya amsa masa, ya ce, “Tashi, ka gangara zuwa Kaila, gama zan ba da Filistiyawa a hannunka.”


Sa'ad da suka kira gare ni, zan amsa musu, Zan kasance tare da su sa'ad da suke shan wahala, Zan cece su in girmama su.


Ku yi kira gare ni sa'ad da wahala ta zo, Zan cece ku, Ku kuwa za ku yabe ni.”


Zai dogara ga Ele'azara, firist, don ya san nufina, ta wurin amfani da Urim da Tummin. Ta haka ne Ele'azara zai bi da Joshuwa da dukan taron jama'ar Isra'ila cikin al'amuransu.”


Saul kuwa ya yi tambaya ga Ubangiji, Ubangiji bai amsa masa ba, ko ta mafarkai, ko ta Urim, ko ta annabawa.


Isra'ilawa suka tashi suka tafi Betel. A can suka yi tambaya ga Allah suka ce, “Wace kabila ce daga cikinmu za ta fara faɗa wa kabilar Biliyaminu?” Ubangiji ya ce, “Kabilar Yahuza ce za ta fara.”


Saul kuwa ya yi tambaya ga Ubangiji, ya ce, “In runtumi Filistiyawa? Za ka bashe su ga Isra'ilawa?” Amma Ubangiji bai amsa masa a wannan rana ba.


Sai ya washe kayayyakin duka, ya kuma ƙwato ɗan'uwansa Lutu da kayayyakinsa da mata da maza.


Magabcin ya ce, ‘Zan bi, in kama su, in raba ganima, Muradina a kansu zai biya, zan zare takobina, hannuna zai hallaka su.’


Ba abin da ya ɓace, ƙanƙane ko babba, ko cikin 'ya'ya mata da maza, ko kuwa wani abu daga cikin ganimar, duk Dawuda ya komar da su.


Da Gidiyon ya zo Urdun sai ya haye tare da mutum ɗari uku ɗin nan da suke tare da shi. Ko da yake sun gaji, duk da haka suka yi ta runtumar magabta.


Suka yi tambaya a wurin Ubangiji, suka ce, “Ko akwai wani dabam?” Ubangiji ya ce, “Ai, ga shi can, ya ɓuya cikin kayayyaki.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ