Bayan wannan sai Dawuda ya roƙi Ubangiji, ya ce, “Ko in haura in mallaki ɗaya daga cikin garuruwan Yahuza?” Ubangiji ya ce masa, “Ka haura.” Dawuda kuma ya ce, “Zuwa wane gari zan haura?” Sai Ubangiji ya ce masa, “Zuwa Hebron.”
Amma Absalom ya aiki manzanni a asirce cikin dukan kabilan Isra'ila a faɗa musu haka, “Da zarar kun ji an busa ƙaho, sai ku ce, ‘Absalom shi ne sarki, yana Hebron.’ ”
Mutanen Yahuza kuwa suka zo, suka naɗa Dawuda da man naɗawa domin ya zama Sarkin Yahuza. Da Dawuda ya ji labari mutanen Yabesh-gileyad, sun binne Saul,
Suka haura ta wajen Negeb, suka isa Hebron inda Ahimaniyawa, da Sheshaiyawa, da Talmaiyawa, zuriyar ƙarfafan mutanen da ake kira Anakawa suke zaune. (An gina Hebron da shekara bakwai kafin a gina Zowan a Masar.)
Kamar yadda Ubangiji ya umarci Joshuwa, ya ba Kalibu, ɗan Yefunne, rabonsa a tsakiyar jama'ar Yahuza. Rabon da aka ba shi, shi ne Kiriyat-arba, wato Hebron. Arba shi ne uban Anak.