Zuriyar Bakene, surukin Musa kuwa suka fita tare da mutanen Yahuza daga birnin dabino, wato Yariko, suka tafi jejin Yahuda da take a Negeb kudu da Arad. A can suka zauna tare da Amalekawa.
Ya ce wa Keniyawa, “Ku tafi, ku rabu da Amalekawa, don kada in hallaka ku tare da su, gama kun yi wa dukan Isra'ilawa karamci lokacin da suka fito daga Masar.” Keniyawa kuwa suka fita daga cikin Amalekawa.