da kuma dukan ƙauyukan da suke kewaye da waɗannan garuruwa tun daga Ba'alat-biyer, wato Ramot ta Negeb. Wannan shi ne rabon gādon iyalan kabilar Saminu.
Joshuwa kuma ya aiki mutane daga Yariko zuwa Ai wadda take kusa da Betawen gabashin Betel, ya ce musu, “Ku tafi ku leƙi asirin ƙasar.” Sai mutanen suka tafi, suka leƙo asirin Ai.
Ya zakuɗa daga nan zuwa dutsen da yake gabashin Betel, ya kafa alfarwarsa, Betel tana yamma, Ai tana gabas, a nan ya gina wa Ubangiji bagade, ya kira bisa sunan Ubangiji.