Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Samaʼila 30:22 - Littafi Mai Tsarki

22 Sai dukan mugaye da marasa kirki daga cikin mutanen da suka tafi tare da Dawuda suka ce, “Tun da yake ba su tafi tare da mu ba, ba za mu ba su kome daga cikin ganimar da muka ƙwato ba, sai dai kowane mutum ya ɗauki matarsa da 'ya'yansa ya tafi.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

22 Sai dukan mugaye da marasa kirki daga cikin mutanen da suka tafi tare da Dawuda suka ce, “Tun da yake ba su tafi tare da mu ba, ba za mu ba su kome daga cikin ganimar da muka ƙwato ba, sai dai kowane mutum yă ɗauki matarsa da ’ya’yansa yă tafi.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Samaʼila 30:22
10 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Saboda haka duk abin da kuke so mutane su yi muku, ku ma sai ku yi musu, domin wannan shi ne Attaura da koyarwar annabawa.”


Sai suka fitar da shi daga cikin birni, suka jajjefe shi da duwatsu har ya mutu.


A kuma sa 'yan iska guda biyu, su yi ta zarginsa, su riƙa cewa, ‘Nabot ya zagi Allah da sarki.’ Sa'an nan ku tafi da shi, ku jajjefe shi da duwatsu har ya mutu.”


Kada maigidana ya kula da Nabal, gama wawa ne, kamar yadda sunansa yake, wato wawa. Ni dai ban ga samarin da ubangijina ya aika ba.


Yanzu sai ki yi tunani, ki san abin da ya kamata ki yi, gama ana niyyar yi wa maigida da dukan gidansa ɓarna. Ga shi, maigida yana da mugun hali, ba zai ji kowa ba!”


Kowane mutum kuma da yake matse, da wanda ake bi bashi, da wanda ransa ba ya kwance, suka tattaru a wurin Dawuda. Shi kuwa ya zama shugabansu. Sun kai wajen mutum ɗari huɗu.


Sa'ad da suke cikin jin daɗin ci da sha, 'yan iskan da suke birnin suka zo suka kewaye gidan, suka yi ta bubbuga ƙofar, suka ce wa tsohon, “Ka fito mana da mutumin da ya zo gidanka don mu yi luɗu!”


Da Dawuda ya zo wurin mutum ɗari biyu ɗin nan waɗanda suka tafke, suka kāsa binsa, waɗanda aka bar su a rafin Besor, sai suka tafi su taryi Dawuda da mutanensa da suka tafi tare da shi. Sa'ad da Dawuda ya zo kusa da su ya gaishe su.


Amma Dawuda ya ce, “'Yan'uwana, ba za ku yi haka da abin da Ubangiji ya ba mu ba. Ubangiji ya kiyaye mu, ya kuma ba da maharan da suka washe mu a hannunmu.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ