16 Amma Eli ya kira shi, ya ce, “Ya ɗana, Sama'ila.” Sama'ila ya ce, “Ga ni.”
16 amma Eli ya kira shi ya ce, “Sama’ila, ɗana.” Sama’ila ya ce, “Ga ni.”
Sama'ila ya kwanta har safiya, sa'an nan ya buɗe ƙofofi. Amma ya ji tsoron faɗa wa Eli wahayin.
Eli ya tambaye shi, ya ce, “Me Ubangiji ya faɗa maka? Kada ka ɓoye mini. Allah zai hukunta ka idan ka ɓoye mini abin da ya faɗa maka.”
Sai mala'ikan Allah ya ce mini a cikin mafarki, ‘Yakubu,’ sai na ce, ‘Ga ni.’
Isra'ila ya ce wa Yusufu, “Ashe, ba 'yan'uwanka suna kiwon garken a Shekem ba? Zo in aike ka wurinsu.” Sai ya ce masa, “Ga ni.”
Sa'an nan sai Bo'aza ya ce wa Rut, “Kin ji, 'yata, kada ki bar wannan gona ki tafi wata gona domin kala, amma ki riƙa bin 'yan matan gidana.
Yanzu ga sarki a gabanku, 'ya'yana maza kuma suna tare da ku. Ni na tsufa, na yi furfura, amma na yi ta kai da kawowa a cikinku tun ina yaro har zuwa yau.