1 Samaʼila 29:3 - Littafi Mai Tsarki3 Shugabannin sojojin Filistiyawa suka ce, “Me waɗannan Ibraniyawa suke yi a nan?” Akish kuwa ya ce wa shugabannin sojojin Filistiyawa, “Ai, wannan Dawuda ne baran Saul, Sarkin Isra'ila, wanda yake tare da ni tun da daɗewa. Tun lokacin da ya zo wurina ban taɓa samunsa da wani laifi ba.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20203 Komandodin Filistiyawa suka ce, “Waɗannan Ibraniyawa kuma fa?” Akish ya ce, “Wannan shi ne Dawuda hafsan Shawulu, sarkin Isra’ila. Yana nan tare da ni shekara guda ke nan. Ban kuwa taɓa samunsa da wani lahani ba tun daga ranar da ya bar Shawulu.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Waɗansu sojoji daga Manassa, suka tafi wurin Dawuda sa'ad da yake fita tare da Filistiyawa don su yi yaƙi da Saul. Amma Dawuda bai tafi tare da su ba, domin sarakunan Filistiyawa sun yi shawara, suka sallame shi, don kada ya juya musu gindin baka, ya nemi sulhu a wurin shugabansu Saul, da kawunansu.